Najeriya ta yi rashi, babban basarake a Katsina ya rasu

Najeriya ta yi rashi, babban basarake a Katsina ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Musawan Katsina, hakimin Musawa, Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman rasuwa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Marigayi Alhaji Muhammad Gidado Usman Liman ya rasu a ranar Laraba, 2 ga watan Satumban 2020 bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita.

Marigayin ya rasu yana da shekaru 77 a duniya kuma ya bar 'ya'ya biyu, Hajiya Binta da Hajia Maijidda, tare da jikoki da 'yan uwa da dama.

Daga cikin 'yan uwansa akwai fitaccen masanin tarihin nan, marigayi Yusuf Bala Usman da kuma dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Musawa da Matazu a tarayya, Ahmad Usman Liman.

Marigayi Muhammad Gidado Usman Liman, jika ne ga Sarki Muhammad Dikko, sarkin masarautar Sullubawa na farko a jihar Katsina.

Hakazalika, marigayin shine hakimi na karshe da Sarki Usman Nagogo ya nada, kakan sarkin yanzu na Katsina.

Tuni aka birneshi kamar yadda addinin Islama ya tanadar a fadarsa da ke Sabon Gari, kwatas din karamar hukumar Musawa.

Najeriya ta yi rashi, babban basarake a Katsina ya rasu
Najeriya ta yi rashi, babban basarake a Katsina ya rasu. Hoto daga Daily Trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Kano: Ina samun a kalla kwastomomi 200 a kowacce rana - Mai bada aron tufafi

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman da sauran hakimai duk suna cikin jiga-jigan da suka halarci jana'izarsa wacce aka yi da karfe biyar na yamma.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, wanda baya jihar a lokacin da aka yi rasuwar, ya karasa garin Musawa a ranar Juma'a.

Ya isa garin tare da mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu da sauran 'yan majalisarsa domin gaisuwar ta'aziyya ga jama'ar garin.

Gwamnan ya kwatanta mutuwar basaraken da babban rashi ba ga jama'ar jihar kadai ba, amma ga dukkan 'yan Najeriya.

Ya ce sarkin mutum ne mai son ganin wanzuwar zaman lafiya kuma mai hangen nesa ne wanda za a yi kewar shawarwarinsa nagari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel