Dole ne a sake zabar Donald Trump idan har ana son zaman lafiya a Amurka - Cewar 'yar Uwar Osama bin Laden

Dole ne a sake zabar Donald Trump idan har ana son zaman lafiya a Amurka - Cewar 'yar Uwar Osama bin Laden

- 'Yar uwar Osama Bin Ladin, Noor Bin Ladin ta nuna goyon bayanta ga shugaba Donald Trump

- Ta ce ta fara goyon bayan Trump tun a shekarar 2015 da ya bayyana kudurinsa na fitowa takara

- Ta ce Trump ne kadai mutumin da zai hana kara kai wani harin na 9/11 a Amurka

'Yar uwar Osama bin Ladin, Noor bin Ladin, ta bayyana cewa Donald Trump shine kawai shugaban kasar Amurka da zai hana wani harin na 9/11 faruwa a kasar Amurka.

Osama bin Ladin shine ya hada harin da aka kai na 9/11 a birnin New York, wannan shine mummunan hari na ta'addanci da aka taba kaiwa kasar Amurka a tarihi.

Noor, wacce ta bayyana cewa tana goyon bayan Trump, wacce kuma ke zaune a kasar Switzerland, ta ce tana goyon bayan Trump tun lokacin da ya fara fitowa takarar shugaban kasa a shekarar 2015.

Dole ne a sake zabar Donal Trump idan har ana son zaman lafiya a Amurka - Cewar 'yar Uwar Osama bin Laden
Dole ne a sake zabar Donal Trump idan har ana son zaman lafiya a Amurka - Cewar 'yar Uwar Osama bin Laden
Source: Facebook

"Na fara goyon bayan Trump tun lokacin da ya bayyana cewa zai fito takarar shugaban kasa a shekarar 2015. Na tsaya nayi nazari a kanshi, kuma nayi na'am da kokarin shi," ta bayyanawa jaridar New York Post a hirarta ta farko da ta fara yi.

"Dole ne a sake zabar shi yana da matukar muhimmanci ga kasar Amurka dama yankin Turai baki daya."

"ISIS za su iya shigowa yankin Turai a karkashin gwamnatin Obama/Biden," cewar matar mai shekaru 33.

KU KARANTA: An yankewa wani mutumi hukuncin kisa bayan an tsinci gawarwakin wasu mata guda biyu a cikin firjin shi

"Trump ya nuna cewa zai iya kare Amurka damu baki daya daga hare-haren ta'addanci tun kafin su kawo inda muke ma."

A watan Afrilu, wasu takardu sunyi ta yawo suna nuna Osama bin Ladin zai kashe shugaban kasa Barack Obama, saboda Joe Biden ya zama shugaban kasa.

"Abinda ya saka suka mai da hankali a wajensu shine, Obama shine shugaba a lokacin, kuma kashe shi zai saka Biden ya zama shugaban kasa," bin Ladin ya rubuta haka a takardar shi.

"Biden a lokacin bai shirya ba, inda hakan zai saka Amurka ta fada cikin rikici."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel