Fargabar kawo hari: An tsaurara matakan tsaro a Abuja da kewaye

Fargabar kawo hari: An tsaurara matakan tsaro a Abuja da kewaye

Hedikwatar rundunar tsaro ta kasa (DHQ) ta sanar da cewa ta tsaurara matakan tsaro a Abuja da wasu makwabtan jihohi bayan samun labarin cewa kungiyar Boko Haram tana shirin kai wasu hare-hare.

DHQ ta ce ta gaggauta daukan wannan mataki ne bayan hukumar kwastam ta Najeriya (NCS) ta fitar da wata sanarwa domin ankarar da mazauna Abuja da wasu makwabtan jihohi a kan shirin kai hare-haren.

Manjo Janar John Enenche, kakakin DHQ, ya ce rundunar soji ta sanar da dukkan dakarunta su kasance cikin shirin 'ko ta kwana'.

A cikin wata sanarwa da hukumar Kwastam ta fitar, ta ce mayakan kungiyar Boko Haram suna shirin kaddamar da wasu hare-hare a Abuja, jihar Kogi da kuma jihar Nasarawa.

Sai dai, a cikin jawabin da Enenche ya fitar ranar Lahadi, DHQ ta bayyana cewa za ta yi kokarin dakile kai hare-haren.

Fargabar kawo hari: An tsaurara matakan tsaro a Abuja da kewaye
Fargabar kawo hari: An tsaurara matakan tsaro a Abuja da kewaye
Source: Facebook

Enenche ya kara da cewa tuni rundunar soji ta ta fara daukan wasu matakan gaggawa da suka hada da tattara bayanan sirri domin ganin cewa burin masu shirin kai harin bai cika ba.

DUBA WANNAN: Da ma can an dora Najeriya a kan turbar shan wuya - Samusi II ya yi magana a kan janye tallafin man fetur

"Hedikwatar rundunar tsaro ta na bawa mazauna Abuja da makwabtan jihohi tabbacin cewa an ankarar da dukkan dakarun soji su kasance cikin shirin mayar da martani a kan duk wani hari da 'yan ta'dda, makiya kasa ke shirin kai wa.

" Yin hakan ya zama wajibi sakamon samun wata takakarda daga hukumar kwastam wace ke gargadin mazauna Abuja da sauran jihohin biyu a kan shirin 'yan Boko Haram na kai wasu hare-hare," a cewar wani bangare na jawabin.

Kazalika, ya bayyana cewa rundunar soji za ta cigaba da hada kai tare da yin aiki da sauran hukumomin tsaro domin kawo karshen aiyukan ta'addanci.

A karshe ya bukaci jama'a su gaggauta sanar da rundunar soji ko kuma jami'an tsaro mafi kusa duk al'amuran wasu batagari domin gaggauta daukan mataki a kan lokaci, ba sai lokaci ya kure ko bayan sun tafka barna ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel