Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari Kajuru, mutum 2 sun rasu, an yi awon gaba da 5

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari Kajuru, mutum 2 sun rasu, an yi awon gaba da 5

Wasu 'yan bindiga da ake zargin makiyaya ne a ranar Lahadi, sun kai hari yankin Adara da ke Buda a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna. Sun kashe Rabaren Alubara Audu da wasu mutum biyu tare da sace wasu mutum biyar.

Awemi Dio Maisamari, shugaban kungiyar kabilar Adara, a wata takarda ya jajanta aukuwar lamarin a yankin sannan ya yi kira ga hukumomi da su kawo karshen lamarin.

Kamar yadda Maisamari yace, "mugun harin da aka kai ya lashe rayukan mutum uku. Sun yi garkuwa da wasu mutum biyar a yankin.

"Wurin daidai wannan lokacin, 'yan ta'addan sun yi garkuwa da mutum biyar daga yankin Kemara Rimi a gundumar Buda."

A ranar Lahadi 16 ga watan Augustan 2020, an kai wani hari a kauyen Kalla da ke kusa da kogin Kaduna. Hakan ya janyo mutuwar wani mutum mai suna Danladi Abashi mai shekaru 50.

An samo gawarsa da taimakon 'yan sanda saboda hana makiyaya shiga yankin Adara da aka yi, jaridar Vanguard ta wallafa.

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari Kajuru, mutum 2 sun rasu, an yi awon gaba da 5
Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari Kajuru, mutum 2 sun rasu, an yi awon gaba da 5. Hoto daga Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA: Maigadi ya rasu bayan ya sha giya sannan ya kwanta da takunkumin fuska

A wani labari na daban, dakarun rundunar Operation Sahel Sanity sun kashe 'yan bindiga biyu, sun damke 12 daga ciki tare da ceto wasu jama'a masu yawa da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Zamfara a makon da ya gabata.

Wannan na kunshe ne a wata takardar da mukaddashin daraktan yada labarai na hukumar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya fitar a ranar Litinin. Onyeuko ya ce, "A ranar 28 ga watan Augustan 2020, dakarun sojin Najeriya da ke Maru sun kai wa wasu da ake zargin 'yan bindiga samame yayin da suke kokarin shiga kauye Gobirawa.

"Cike da kwarewar dakarun tare da taimakon 'yan sa kai, sun hana 'yan bindigar shiga kauyen.

"A yayin samamen, dakarun sun yi musayar wuta da 'yan bindigar inda suka kashe biyu daga ciki, amma wasu sun tsere da miyagun raunika. An ga jini a kasa wanda ya bayyana hanyar da suka bi.

"A wannan ranar, dakarun sun kai samame wata maboyar 'yan bindigar da ke kauyen Gamji. A yayin samamen, an kama 'yan bindiga shida sannan an samo bindiga daya, babur daya da adduna biyu.

“Dakarun sojin da aka kai Zakka, sun damke wasu 'yan bindiga uku bayan bayanan sirri da suka samu. Sun damke Sagir Garba, Hafizu Mato da Suleiman Sada."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel