Mutum 4 ƴan gida ɗaya sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Mutum 4 ƴan gida ɗaya sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Mutane huɗu ƴan gida ɗaya sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyan Kano zuwa Jigawa a ranar Asabar.

Wani ɗan uwan wadanda suka rasu, Shehu Yusuf Kazaure ya ce dukkan wadanda suka mutu ƴan gidan Hajiya Safiya Mohammed ce, direktan Ilimin gaba da sakandare a ma'aikatar Ilimi na jihar.

Suna kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar Malam Madori ne ɗaurin aure yayin da motarsu ta yi Kundin bala a kusa da Danladin-Gumel a ƙaramar hukumar Gumel.

Mutum huɗu ƴan gida ɗaya sun mutu a haɗarin mota a Jigawa
Mutum huɗu ƴan gida ɗaya sun mutu a haɗarin mota a Jigawa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

"Hadarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar.

"Uku cikin yaran Hajiya Safiya; Fati, Abba da Zainab sun mutu nan take.

"An tafi da su Malam Madori. Amma ko da suka isa can, Hanan, ɗiyar Zainab ita ma ta cika.

"Abin baƙin ciki ne ga iyalan domin yawancin mu mun zubar da hawaye.

"Mutuwar mutum huɗu ƴan gida ɗaya a rana guda ba ƙaramin lamari bane.

"Lallai abin baƙin ciki ne, ina addu'ar Allah ya gafarta musu," in ji Kazaure.

Ya ce an yi musu jana'iza a Malam Madori bisa koyarwar addinin musulunci.

A wani labarin daban kun ji hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Kano (SEMA) ta tabbatar da cewa ambaliyar ruwa ta kashe mutum huɗu tare da lalata gidaje fiye da 5,200 a Rogo da ke ƙaramar hukumar Danbatta na jihar.

Sakataren hukumar, Mista Sale Jili ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Asabar a Kano.

NAN ta ruwaito cewa hukumar kula da yanayi ta kasa, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a wasu ƙananan hukumomi 20 a jihar Kano.

Jili ya bayyana cewa mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya yayin da gidaje 200 sun lalace a Rogo yayin da wasu mutum biyu sun mutu a Danbatta kuma ruwar ta lalata gidaje 5,000.

"Mun aike da tawagar mu da za su duba abinda ya faru a wuraren. Mun kuma ziyarci Rogo da Danbatta domin jajanta wa mutanen da iftila'in ya shafa.

"Akwai rahotannin ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi 44 na jihar saboda ruwan sama mai yawa da aka samu a bana," in ji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel