Kano: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum huɗu, ta lalata gidaje masu yawa

Kano: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum huɗu, ta lalata gidaje masu yawa

Hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Kano (SEMA) ta tabbatar da cewa ambaliyar ruwa ta kashe mutum huɗu tare da lalata gidaje fiye da 5,200 a Rogo da ke ƙaramar hukumar Danbatta na jihar.

Sakataren hukumar, Mista Sale Jili ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai, NAN, a ranar Asabar a Kano.

NAN ta ruwaito cewa hukumar kula da yanayi ta kasa, NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a wasu ƙananan hukumomi 20 a jihar Kano.

Kano: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum huɗu, ta lalata gidaje masu yawa
Kano: Ambaliyar ruwa ta kashe mutum huɗu, ta lalata gidaje masu yawa. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

Jili ya bayyana cewa mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya yayin da gidaje 200 sun lalace a Rogo yayin da wasu mutum biyu sun mutu a Danbatta kuma ruwar ta lalata gidaje 5,000.

"Mun aike da tawagar mu da za su duba abinda ya faru a wuraren. Mun kuma ziyarci Rogo da Danbatta domin jajanta wa mutanen da iftila'in ya shafa.

KU KARANTA: Sun mayar da mu karuwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya

"Akwai rahotannin ambaliyar ruwa a ƙananan hukumomi 44 na jihar saboda ruwan sama mai yawa da aka samu a bana," in ji shi.

A cewarsa, a halin yanzu mutanen da suka rasa muhallan su suna fake wa a gidajen ƴan uwansu a garuruwan su.

Jili ya ce hukumar ta raba kayan tallafi da kudin su ya kai Naira miliyan 3.5 ga wadanda abin ya shafa don rage musu raɗaɗin asarar da suka yi.

Ya lissafa cewa abubuwan da aka raba wa mutanen sun hada da buhunnan siminti, barguna, katifu, sabulai da wasu kayayyakin.

Sakataren ya bukaci mutane su riƙa gyara magudanan ruwa kuma su guji zubar da shara a kwata da hanyoyin ruwa don takaita ambaliyar ruwa a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel