Wani binciken masana kimiyya ya nuna kayan kamshi da ake farfesu dashi na iya maganin cutar korona

Wani binciken masana kimiyya ya nuna kayan kamshi da ake farfesu dashi na iya maganin cutar korona

Wani bincike da masu binciken kimiyya suka gudanar ya nuna cewa Kimba da ake kira (Ethiopian pepper ko Negro Pepper) yana hana ƙwayar cutar coronavirus virus shiga jikin ɗan adam.

Ƙwayar cutar ta coronavirus na bukatar wani sashi a jikin ƙwayar hallitar ɗan adam da zai yi amfani da shi wurin shiga cikin ƙwayar hallita da ke kira angiotensin-converting enzyme 2.

Shi kansa ƙwayar cutar yana da wata sinadari na kansa, protease da ke taimaka masa wurin hayayyafa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kayan ƙamshi na yin farfesu na iya magananin cutar korona - Binciken masana
Kayan ƙamshi na yin farfesu na iya magananin cutar korona - Binciken masana. Hoto daga Nigerian Food Tv
Source: Twitter

Masu bincike sun wallafa a wata takarda daga Razi Institute inda suka nuna cewa Kimba na ɗauke da wasu sinadarai da ke iya hana ƙwayar cutar coronavirus shiga cikin ƙwayar hallitar ɗan adam cikinsu har da elagic acid da xylopic acid.

A harshen Ibo ana kiran Kimba da suna Uda, yarabawa kuma suna kiran sa Erunje ko Erinje kuma ana amfani da shi wurin yin magungunan gargajiya da dama.

Ana kuma amfani da shi a matsayin kayan ƙamshi ɗon ƙarin ɗanɗano a abinci ko ƙara ƙamshi.

Wasu tsirran da masanan suka ce ana iya gwaji da su sun hada da citta, lemu, thyme da itacen roba.

KU KARANTA: Hotuna: Ƙaramin yaron da al'umma suka bawa tallafin kuɗi ya buɗe 'katafaren kanti' a Kano

Tawagar masu binciken sun hada da Dakta B.J. Iso (shugabansu), Dakta S.O. Omeika da I.O. Olaoye duk malamai ne a Tsangayar nazarin kimiyyar abubuwa masu rai a Jami'ar McPherson.

Masanan sun gwada yadda sinadaran da ke cikin Kimba (resveratol, xylopic acid, ellagic acid, kaempferol da quercetin) ke toshe wurin da ƙwayar cutar ke bi wurin shiga cikin ƙwayar hallita a jikin ɗan adam.

Sun gano cewa wasu daga cikin sinadaran sun fi chloroquine ƙarfin hana ƙwayar cutar shiga cikin jiki ta hanyar amfani da Pyrex Virtual Screening tool.

Sun yi hasashen yadda sinadaran za su yi aiki wurin dakile ƙwayar cutar ta hanyar amfani da admetSAR.

Hasashen na Admet ya nuna cewa sinadaran ba su da hatsari kamar chloroquine kuma za a iya amfani da su wurin hana kwayar cutar SARS-CoV-2 shiga cikin ɗan adam da hayayyafa.

Sai dai sun janyo hankalin mutane cewa hasashe ne suka yi amma akwai bukatar a shiga ɗakin gwaji a zurfafa bincike.

"Wannan sakamakon da muka samu yana iya zama makami da zamu iya amfani da shi wurin yaƙi da coronavirus,' in ji masu binciken.

"Wannan binciken da muka yi zai zama kamar wani haske ne ga masu zurfafa bincike don sanin inda za su mayar da hankali.

"Tsirai suna da sinadarai da dama masu amfani da suka hada da na kare mu daga kamuwa daga cututtuka," in ji Omeike.

"Amma akwai buƙatar a tace sinadarin kuma ayi bincike a kan tabbatar da ba zai haifar da wani matsala ba a jiki kafin wasu masu magungunan gargajiya su fara yin jiƙo da shi suna bawa mutane".

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel