Matar aure ta cafke mazakutar mijinta da hakora, ta bar shi rai sama-sama

Matar aure ta cafke mazakutar mijinta da hakora, ta bar shi rai sama-sama

Abraham Musonda mai shekaru 52 a duniya ya fada wani mummunan hali da matarsa mai shekaru 40 ta jefa shi sakamakon kin cire mata bera da yayi daga kusa da gadonta.

Mukupa da mijinta an gano suna zama ne a wani birnin kasar Zambia mai suna Kitwe. Ta hari mijinta bayan da suka samu hargitsi a kan bera.

Ta yi ikirarin cewa beran yana tsorata ta, kuma ta yi matukar fusata bayan da ta dawo gida ta tarar da shi a kusa da gadonta.

Sakamakon kaiwa da kawowar beran, Mokupa ta kasa bacci kuma ta umarci mijinta da ya san yadda zai yi da beran da take tsoro.

Rikici ya barke tsakanin ma'auratan bayan da ya ki fitar da beran, lamarin da yasa ta cafke mazakutarsa tare da gannara masa mugun cizo.

Cizon da ta yi masa kuwa ya janyo mummunan ciwon da yayi barazanar tsinke masa mazakuta.

Bothwell Namuswa, mataimakin kwamishinan 'yan sandan yankin Copperbelt, ya sanar da cewa ma'auratan sun rabu amma suna zama a gida daya.

Kamar yadda jaridar Metro UK ta wallafa, an gaggauta mika Musonda asibitin koyarwa na Kitwe domin samun agajin gaggawa.

Matar aure ta cafke mazakutar mijinta da hakora, ta bar shi rai sama-sama
Matar aure ta cafke mazakutar mijinta da hakora, ta bar shi rai sama-sama. Hoto daga Vanguard
Source: UGC

KU KARANTA: Bauchi: Sojoji 2 sun rasu, 1 yana kwance rai a hannun Allah bayan hatsarin mota

A wani labari na daban, wani mutum mai shekaru 41 mai suna Ogbonna Nwankwo, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Anambra a kan zarginsa da ake yi da yunkurin kashe wata mata mai suna Bella Joseph tare da cire mata nonuwa a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba.

A yayin bayani ga manema labarai, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed, ya ce Ogbonna ya kai Bella otal din Dollar Inn Motel da ke Ihite a karamar hukumar Orumba ta kudu.

Ya ce a yayin da suka shiga dakin otal din, wanda ake zargin ya yi amfani da wuka inda ya sokawa Bella kuma ya fara yunkurin cire mata nonuwa.

Ihun neman taimakon da ta fara yi ne ya janyo hankalin manajan otal din wanda ya gaggauta zuwa dakin.

"Ana zargin wani mutum da yunkurin kashe wata budurwa a cikin dakin otal ta hanyar soka mata wuka tare da yunkurin cire mata nononta na dama.

"Ana zargin ya yi wannan yunkurin ne domin tsafi da matar kafin ta yi ihu, inda ta samu taimako daga manajan otal din." yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel