DPO ya kama wadanda su ka dauke kajin mutane a Bauchi, ya kashe su da duka

DPO ya kama wadanda su ka dauke kajin mutane a Bauchi, ya kashe su da duka

Jaridar Daily Trust ta fitar da cikakken labari na wani jami’in ‘yan sanda da ya kashe mutane biyu a dalilin zarginsu da ake yi da laifin satar kaji a Bauchi.

Kwanakin baya dakarun ‘yan sanda su ka kama Ibrahim Kapala, Ibrahim Babangida da Abdulwahab Bello, a karshe 'yan sanda su ka yi sanadiyyar mutuwarsu.

Rahoton da aka fitar ya ce ana zargin DPO Baba Ali Mohammed ne ya yi ta dukan wadannan Bayin Allah, a sanadiyyar haka ne su ka ce masa ga garin ku nan.

Abdulwahab Bello wanda yanzu an karya masa duka kafafunsa shi ne ya taki sa’a, amma kwanakin abokansa sun kare a hannun wannan mugun jami’i, Baba Ali.

Jami’an tsaro sun yi ram da wadannan mutane uku ne da sunan sun saci kajin wani tsohon ‘dan sanda da ya yi ritaya. Laifin Bello shi ne ya hada su da mai sayen kajin.

Abdulwahab Bello ya ce bai san cewa kajin sata ake neman saidawa ba. Bayan ya raka Kapala da Babangida zuwa kasuwa, sai ga ‘yan sanda su na binsu a Keke Napep.

A nan aka cafke Bello aka yi gaba da shi zuwa ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Doya, jami’an ‘yan sandan sun kuma cafke wanda ya saye wadannan kaji biyar na sata.

Mai dukiyar ya zargi matasan da sace masa kaji 24, daga baya ya ce ya gano 13 daga ciki. DPO Baba Ali ya bukaci matasan su biya kudin kajin da kuma kudin belinsu.

KU KARANTA: Ambaliya ta kashe mutane 5 a wani Kauye a Bauchi

DPO ya kama wadanda su ka dauke kajin mutane a Bauchi, ya kashe su da duka
Abdulwahab Bello wanda ya yi rai Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Bello ya ce mahaifiyarsa ta biya N4, 000 a matsayin kudin kajin da aka sace, amma DPO ya nemi a kara biyan N2, 000 na beli, da aka gaza biyan wannan kudi, ya tsare su.

Da aka tsare wadannan mutane sai DPO ya bada umarnin daure Ibrahim Kapala, shi kuwa ya yi ta bugunsa da karyayyen tabarya, a nan ya karya masa kafafu su na ji, su na gani.

“A nan ya ke cewa daga yau an daina satar kaji, wajen dukansa har ya suma, shi kuma ya cigaba da bugunsa da kafa har sai dai ya mutu.” Inji Bello da ya yi rai.

“Nan take ya sa aka kawo dayan wanda ake zargi, ya kama shi da duka ya karya masa kafafu da wannan tabarya dai, ya yi amfani da ita ya gwabje shi a kirji da bayansa.”

DPO ya sumar da wannan Bawan Allah shi ma.

“Da aka zo kai na, ya sa mani wannan tabarya, har sai da ya karya mani kafafu, na samu karaya biyu a kafa guda.”

Daga nan ne aka zuba su a cikin mota, aka je gidan Ibrahim Kapala, DPO ya karasa mauje shi a kai, aka jefar da gawarsa, aka fadawa ‘yanuwansa cewa ‘dan fashi ne shi.

Shi ma haka aka yi wa Babangida, har yanzu ‘yanuwansa su na jimamin abin da ya faru.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel