2023: Muhammad Sanusi II ya yi magana a kan burinsa na siyasa

2023: Muhammad Sanusi II ya yi magana a kan burinsa na siyasa

Muhammadu Sanusi, tsohon sarkin Kano, ya ce bashi da wani buri na fitowa takarar kujerar siyasa a kasar nan. A yayin da zaben 2023 ke gabatowa, ana ta hasashen 'yan takara da za su bayyana kafin zaben.

A wata tattaunawa da basaraken ya yi da Arise TV a ranar Juma'a, Sanusi ya ce bashi da ra'ayin siyasa kwata-kwata.

Tsohon basaraken ya ce zai koma karatu a fitacciyar jami'ar Oxford da ke Ingila a watan Oktoba mai zuwa.

Hukumar kwamitin cibiyar Afrika ta makarantar, ta amince da bukatar Sanusi na komawa karatun.

Tsohon basaraken ya ce yana da niyyar komawa malumta, wanda daga nan ya fara rayuwarsa.

"Jama'a suna ta yi min magana a kan siyasa tun a lokacin da nake babban bankin Najeriya. Ban taba ra'ayin siyasa ba har yanzu.

"Yanayin gidan da na fito shine, muna kallon kanmu a matsayin shugabannin talakawa kuma kun san siyasa bata dace da hakan ba," yace.

"Abinda zan iya cewa shine, wannan ba ita bace manufata. Ina tunanin akwai hanyoyin bautawa kasa.

"Na fara a matsayin malamin makaranta. Bayan shekaru biyu da na kammala digirina na biyu, sai na fada bangaren banki. Na kasance ma'aikacin banki kuma daga baya basarake."

2023: Muhammad Sanusi II ya yi magana a kan burinsa na siyasa
2023: Muhammad Sanusi II ya yi magana a kan burinsa na siyasa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da ya yanke wa budurwa nonuwa a otal (Hotuna)

Sanusi ya ce yana da burin wallafa litattafai uku yayin da yake jami'ar Oxford kuma daya daga ciki zai yi magana ne a kan shari'a.

Daya kuwa zai mayar da hankali ne wurin magana a kan yadda babban bankin Najeriya ke daukar mataki a kan rikicin kudi.

Ya ce littafin na uku zai rubuta shi ne a kan yadda Musulmai ke fassara wasu dokoki da kuma al'adu, wanda hakan ke kawo rashin ci gaba a arewacin Najeriya.

"Akwai yuwuwar in koma aikina na farko da ban kammala ba har yau. Zan iya zama farfesa a jami'o'i daban-daban.

"Babban abinda nake da shi shine, ba kowacce jami'a bace take da mutum mai digirin digirgir, tsohon shugaban banki kuma basarake ba," yace.

"Wannan takardun nawa za su iya samo maka kowacce irin jami'a a duniya, koda kuwa Harvard, Oxford, Cambridge da sauransu ne.

"Bana iya ganin abinda zai faru a gaba, don haka zan rungumi rayuwa yadda take tahowa. Ba sauri nake yi ba.

"A gaskiya ina ganin kaina a matsayin mai hidimtawa jama'a, amma bana tunanin ofishin siyasa ba zai durkusar da ni ba." yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel