Alkawari ya cika, an daura auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban (Hotuna)
- Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Hanan Buhari, ta tabbata matar Muhammad Turad Sha'aban
- Tuni hotunan bikin 'yan gatan ya karade kafofin sada zumuntar zamani
- Mahaifiyar amarya, Aisha Buhari, cike da farin ciki ta wallafa hotunan ango da amaryar a shafinta na Instagram
Babu shakka ranar 4 ga watan Satumban 2020 babbar rana ce ga iyalan shugaban kasa Najeriya, Muhammadu Buhari.
Sun mika auren diyarsu a fadar shugaban kasar Najeriya da ke fadar Aso Rock a Abuja.
Tuni sakonnin sam barka da taya murna ya karade kafofin sada zumuntar zamani ga Hanan Buhari da kyakyawan angonta, Muhammad Turad Sha'aban, a yayin da suka zama mata da miji.
Muhammad Turad Sha'aban da ne ga tsohon dan majalisar wakilai da ya taba wakiltar mazabar Sabon Gari a Zaria.
Alhaji Mahmud Sha'aban tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna ne a zaben 2007 da na 2011.
Alhaji Sha'aban na rike da sarautar Damburam na masarautar Zazzau.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Turad kwararre ne a harkar kudi kuma mai bada shawara na musamman ne ga tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Fashola.
Hanan ta kammala digirinta a fannin daukar hoto daga jami'ar Ravensbourne da ke Ingila.
KU KARANTA: Dumu-dumu: An kama wani mutum yayin da ya yanke wa budurwa nonuwa a otal (Hotuna)
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng