Mutumin Neja ya cusa sunan ‘danuwansa a Ma’aikatan bogi har na tsawon shekaru 11

Mutumin Neja ya cusa sunan ‘danuwansa a Ma’aikatan bogi har na tsawon shekaru 11

Wani babban ma’aikacin gwamnatin jihar Neja, Mohammed Ndanusa, ya shiga hannun jami’an tsaro bayan an same shi da laifin cin albashi wani.

Alhaji Mohammed Ndanusa ya cusa sunan wani ‘danuwansa a jerin ma’aikatan gwamnatin Neja, kuma ya na ta karbar albashin wannan Bawan Allah tun 2009.

Mohammed Ndanusa wanda ya ke aiki da ma’aikatar lafiya ta jihar ya yi shekaru 11 ya na karbar albashi da sunan wannan ‘danuwan sa kafin a kama shi.

Wani bincike da gwamnati ta ke yi ne ya tona asirin Mohammed Ndanusaa a ranar Talatar nan kamar yadda mu ka samu labari daga shafin Reuben Abati.

A lokuta dabam-dabam, Ndanusa ya yi ta kara matsayi ga wannan ma’aikacin bogi da ya kawo, wanda sai da ya kai matakin aiki na 14 kafin asirinsa ya tonu.

Abin mamakin shi ne wanda aka dauki aikin da sunansa, Tanimu Ndanusa ya na cikin garin Minna ya na acaba da babur, bai cancanci ya yi aikin gwamnati ba.

KU KARANTA: Sakamakon jarrabawar PQE na Malaman Makaranta ya fito

Mutumin Neja ya cusa sunan ‘danuwansa a Ma’aikatan bogi har na tsawon shekaru 11
Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello
Asali: UGC

Abubuwa sun cabewa Mohammed Ndanusa ne a lokacin da aka bukaci Tanimu Ndanusa ya hallarci zaman kwamitin da ke tantance ma’aikatan gwamnatin Neja.

Da wannan ‘Dan acaba ya bayyana gaban kwamitin kamar yadda aka bukaci kowane ma’aikaci ya zo, sai aka ga cewa Tanimu Ndanusa bai da wasu takardun shaida.

Bayan haka Malam Tanimu Ndanusa bai yi kama da babban jami’in gwamnati da har ya kai mataki na 14 a ofis ba. Nan take jami’an da ke bincike su ka kira ‘yan sanda.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Mohammed Ndanusa da Tanimu Ndanusa su na hannun jami’an tsaro, kuma da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu.

Shi dai Mohammed Ndanusa tuni ya amsa laifinsa, ya ce shi ya jefa sunan ‘danuwansa a cikin ma’aikatan bogi, sannan har ya kara masa matsayi sau uku a wannan lokaci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel