‘Yan kasuwa sun ce akwai yiwuwar litar man fetur ya kuma kara tsada

‘Yan kasuwa sun ce akwai yiwuwar litar man fetur ya kuma kara tsada

- Ana hasashen gangar danyen mai zai cigaba da kara kudi a Duniya

- Wannan zai sa litar man fetur ta kara tsada a gidajen man Najeriya

- Farashin litar man fetur ya tashi daga N125 zuwa N160 a wata uku

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu saida man fetur a gidajen man da ke fadin Najeriya sun canza kudin lita a ranar Alhamis zuwa tsakanin N158 da N162.

Watanni uku kenan aka dauka farashin man fetur ya na tashi, daga N121-N123 a watan Yuni, zuwa N140-N143 a Yuli, sai kuma yanzu da litar ta koma N158-N162.

Jaridar Punch ta ce karyewar darajar danyen mai a kasuwannin Duniya ne ya jawo gwamnatin Najeriya ta yi kasa da farashin litar fetur zuwa N125 a watan Maris.

‘Yan kasuwa da dillalan man fetur a Najeriya sun ce akwai yiwuwar lita ta kara kudi nan gaba, idan aka yi la’akari da yadda danyen mai ya ke kara daraja a kasuwa.

KU KARANTA: Tsadar abinci: Shugaba Buhari ya tona asirin masu laifi

‘Yan kasuwa sun ce akwai yiwuwar litar man fetur ya kuma kara tsada
Gwamnati ta ce karin kudin man fetur ya fi karfin Buhari
Source: Twitter

Shugaban manyan dillalan mai, Adetunji Oyebanji, ya tabbatar da cewa farashin gidajen mai zai canza tun da har kudin da ake saida fetur ya tashi a manyan tashoshi.

Mista Adetunji Oyebanji ya ce ba za su kayyadewa kamfanoni kudin da za su saida man fetur din ba, yanayin wurin da gidan mai ya ke ya na da tasiri da farashin litarsa.

Shugaban kungiyar ta MOMAN ya ji dadin yadda gwamnati ta kyale kasuwa ta tsaida farashi, ya ce abin a yaba da wannan mataki ne da hukumomin kasar su ka kawo.

Cire hannun gwamnati wajen tsaida farashi zai sa a daina biyan tallafin mai, sannan mutane da-dama za su samu aikin yi, kuma ‘yan kasuwan kasar za su fi samun riba.

Da zarar gangar danyen mai ya kara kudi a Duniya, farashin man fetur zai sake rikida, a halin yanzu da mai ke kara daraja, mutane su rika tsammanin karin farashin lita.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel