Bidiyo: Sai dana yi kwanaki 14 ba abinci sai ruwan kashi da nake sha kawai akan hanyar zuwa Libya - Budurwa

Bidiyo: Sai dana yi kwanaki 14 ba abinci sai ruwan kashi da nake sha kawai akan hanyar zuwa Libya - Budurwa

- Wata budurwa 'yar Najeriya mai suna Omolara Akintayo, ta ce tayi dana sanin zuwa kasar yankin Arewacin Afrika

- Budurwar mai shekaru 24 ta ce ta tafi kasar ta Libya ne domin neman arziki, saboda iyayenta na zaune cikin talauci

- A cewarta, abubuwa da yawa marasa dadin ji sun faru akan hanyarta ta zuwa Libya, ciki kuwa hadda shan ruwan kashi

Wata budurwa mai shekaru 24 da aka bayyana sunanta da Omolara Akintayo ta ce tayi dana sanin zuwa kasar Libya neman arziki.

A wata hira da tayi da Legit TV, matashiyar budurwar ta ce ta tafi kasar ta Libya ne saboda iyayenta na cikin matsanancin hali na talauci.

Omolara ta bayyana irin halin da ta shiga akan hanyarta ta zuwa kasar ta Libya, inda ta ce ta shafe kwanaki 14 akan hanya kafin su karasa kasar.

Bidiyo: Sai dana yi kwanaki 14 ba abinci sai ruwan kashi da nake sha kawai akan hanyar zuwa Libya - Budurwa
Bidiyo: Sai dana yi kwanaki 14 ba abinci sai ruwan kashi da nake sha kawai akan hanyar zuwa Libya - Budurwa
Source: UGC

A cewarta, a lokacin da suke tsakiyar sahara, da yawa daga cikin mutane sun mutu, wasu kuma an sanya su dole suka sha ruwan kashi, saboda babu ruwa mai kyau ko abinci.

Omolara ta ce biyu daga cikin kawayenta anyi musu fyade a tsakiyar sahara akan hanyarsu ta zuwa Libya.

Ta ce: "Abubuwa da yawa sun faru akan hanyar mu. Inda ace na san da su kafin na bar Najeriya, babu yadda za ayi na tafi Libya."

Omolara ta ce abubuwa marasa kyau da sun faru da ita da wasu daga cikin abokanan tafiyarta in ba dan kariyar Allah ba.

Ta ce: "Lokacin da muka isa Libya na biya mutumin da ya kai ni can N600,000 a cikin shekara daya."

KU KARANTA: Mutumin da wani magidanci ya kira su taru su ladabtar da danshi ya cakawa yaron wuka

Budurwar ta ce mutumin da ta biya wannan kudi shine ya gudu ya bar ta a gidan wani Balarabe, inda aka hana ta fita tsawon shekara daya.

Ta ce: "Wannan mutumin shine yake karbar albashina kowanne wata, yayin da ni kuma nake aikin. Na kasa cin komai a can saboda bana iya cin abincin su.

"Wani lokacin ina kwanciya bacci da karfe 2 ko 3 na dare, saboda sai na wanke kwanikan abinci. Wani lokacin mu wanke musu kashi, mu sanyawa tsofaffi kaya. Babu abinda bamu yi ba, abubuwan da inda a gida nake ko iyayena baza su saka ni nayi musu ba, amma nayi su a can."

Budurwar ta ce tana ganin laifinta ne akan halin da ta shiga a Libya, ta ce sai da ta shafe shekara biyu bata yi magana da iyayenta ba.

Ta ce lokacin da ta samu matsala a wajen aikinta, an tambayeta idan za ta shiga harkar karuwanci, ta ce a'a zai fi tayi aikin goge-goge.

Omolara ta ce: "Na cigaba da aiki a matsayin mai shara da wanke-wanke a gidan mutumin na tsawon shekara biyu, ina kulle babu inda nake fita, haka kuma ban san lokacin da wancan mutumin yake zuwa yana karbe albashina ba."

Ta ce ta samu 'yanci ne bayan ta biya mutumin da ya kai ta Libya din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel