Buhari zai gabatar da sabuwar tsarin tattalin arziki a watan Disamba - Minista

Buhari zai gabatar da sabuwar tsarin tattalin arziki a watan Disamba - Minista

A ranar Alhamis ne Karamin Ministan Kasafi da Tsarin Kasa, Clement Agba, ya bayyana cewar a watan Disamba ne za a gabatar da sabon salon tsarin bunkasa tattalin arzikin kasa wanda zai yi tasiri har tsawon shekaru hudu.

Ministan ya ce Shugaba Buhari ne zai gabatar da wannan tsarin wanda yunkuri ne na farfado da tattalin arziki wanda ya riga ya durkushe a wannan shekarar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ministan ya kara da cewar, tsarin an kasa shi gida biyu, gajeran zango wanda zai yi tasiri tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025 da kuma shekarun 2026 zuwa 2030.

Buhari zai gabatar sabuwar tsarin tattalin arziki a watan Disamba - Minista
Buhari zai gabatar sabuwar tsarin tattalin arziki a watan Disamba - Minista
Asali: Twitter

Sai kuma tsari na dogon zango wanda hasashe ne na shekarar 2050.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnatin Tarayya ta amince da buɗe makarantu a Najeriya

Ministan ya yi wannan jawabi ne a taron karawa juna sani da hukumar ta sa ta shirya. Ya kuma ce wannan tsarin zai sanya Najeriya cikin jerin kasashe guda 20 mafiya arziki a duniya.

"Wannan tsarin shi ne zai yi jagoranci wurin kasafin kasa na shekarar 2021", In ji Ministan.

Har ila yau, Ministan ya kara da cewa, manyan jam'iyyu da majalisun taryayya, da kungiyoyi Manya da kanana na mata matasa duk za su taka rawar gani wurin tabbatar da wannan tsarin.

A wani labarin daban, kun ji dubban 'yan Najeriya sun yi tururuwa wajen bayyana ra'ayinsu tare da mayarwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, martani a kan kara farashin man fetur da kuma tsadar kayan abinci.

Hauhawar farashin kayan abinci da kara farashin litar man fetur da karin kudin wutar lantarki sun harzuka 'yan Najeriya, lamarin da yasa jama'a da dama ke bayyana nadamarsu tare da yin da na sanin goyon bayan gwamnatin Buhari.

A ranar Laraba ne kafafen yada labarai su ka wallafa labarin cewa kamfanin tallar man fetur mallakar gwamnatin tarayya (PPMC) ya sanar da kara farashin litar mana fetur zuwa N151 kowacce lita.

Kafin fitowar sanarwar kara farashin man fetur, hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta kasa (NERC) ta sanar da yin karin kudin wutar lantarki daga N27.2 zuwa N66 a kan kowanne KW a ranar Talata, 1 ga watan Satumba.

Da ya ke martani a kan karin kudin wutar lantarki, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, ya ce ko kadan bai kamata karin kudin ya zo a irin wannan lokaci da jama'a suke a galabaice ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel