Babu yadda Buhari ya iya da karin farashin mai, abin ya wuce ikonsa - Karamin Ministan Mai

Babu yadda Buhari ya iya da karin farashin mai, abin ya wuce ikonsa - Karamin Ministan Mai

Karamin ministan arzikin man fetur, Temipre Sylva, ya ce karin farashin man feturin da aka yi ba yin shugaba Buhari bane saboda dan tashi, ba za a taba kara farashin ba.

A ranar Laraba, kamfanin kasuwancin mai PPMC ta sanar da tashin farashin mai zuwa N151.56.

Bayan haka kuma, yan kasuwan mai zasu kara nasu idan aka fara sayarwa N159 zuwa N162.

Yayin magana da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Temipre Sylva ya ce ba hakkin gwamnatin tarayya bane sanya farashin mai.

Yace akwai takaici yan Najeriya na daura laifin kan gwamnatin tarayya alhalin ita gwamnatin na kokarin kare mutuncinsu

"Gwamnati ta cire hannunta cikin lamarin sanya farashin man fetur, mun janye," NAN ta ruwaitoshi da cewa

"Yanzu mun mayar da hankalinmu ne kan kare mutuncin yan Najeriya wajen tabbatar da cewa yan kasuwa basu samun riba fiye da yadda ya kamata."

"Dukkanku kun san shugaba Muhammadu Buhari mutumin talakawa ne, musamman marasa galihu."

"Dan ta shi, ba zai taba bari a kara farashin man fetur ba, tun da kuka ga hakan ya faru, to abin ya fi karfinsa ne. COVID-19 ce ta karya farashin danyen mai."

Ministan yace an siyasantar da lamarin sashen arzikin mai.

Babu yadda Buhari ya iya da karin farashin mai, abin ya wuce ikonsa - Karamin Ministan Mai
Babu yadda Buhari ya iya da karin farashin mai, abin ya wuce ikonsa - Karamin Ministan Mai
Source: Twitter

KU KARANTA: Jami'o'in Najeriya 6 na cikin manyan jami'o'i 1000 mafi inganci a duniya (Jerinsu)

A bangare guda, Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta daura laifin karin farashin man fetur kan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da gwamnatocinta na baya.

Jam'iyyar mai ci ta yi raddi ne ga PDP yayindata t a caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara farashin mai da na wutan lantarki yayinda yan Najeriya ke cikin halin talauci.

APC ta ce gwamnatocin PDP da suka shude ne suka sace arzikin kasar nan ta hanyar biyan tallafin mai, kuma hakan ke sabbaba matsalan da ake fuskanta yanzu.

Kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel