NAPTIP ta kama Cecilia Onyema, dillaliyar jarirai a unguwar Sabongari

NAPTIP ta kama Cecilia Onyema, dillaliyar jarirai a unguwar Sabongari

- NAPTIP, hukumar da ke yaki da safarar mutane a kasa, ta kama wasu mata da ake zargin suna da hannu a saye da sayar da jarirai

- Jami'an NAPTIP sun kama Cecelia Onyema, wata ma'aikaciyar ma'aikatar noma da raya karkara ta tarayya, da ke zaune a unguwar Sabon Gari da ke Mararaba a jihar Nasarawa

- Ana zargin Cecilia da dillancin jarirai bayan an kamata da laifin sayar da wani jariri a kan N1.5m ga wata mata mai suna Bernette Chinonso Ihezuo

Hukumar da ke yaki da safara da fataucin mutane a kasa (NAPTIP) ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu a kasuwancin saye da sayar da jarirai a yankin Mararaba da ke jihar Nasarawa.

Babbar darekta a hukumar NAPTIP, Julie Okah-Donli, ce ta sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja.

A cewarta, jami'an NAPTIP sun samu nasarar kama wata mata Cecila Ugbaku Onyema, ma'aikaciya a ma'aikatar noma da raya karkara ta tarayya, wacce ake zargi da zama dillaliyar da ke sayar da jaririai.

Julie ta bayyana cewa jami'an NAPTIP sun kama Cecelia a wani gida mai lamba 1314 da ke kan titin Bridget a unguwar Sabon Gari da ke yankin Mararaba a jihar Nasarawa bayan samun sahihan bayanan sirri.

Shugabar ta NAPTIP ta sanar da cewa sun kubutar da wata matashiya mai shekaru 16 wacce aka yi safararta daga jihar Imo kuma ta zo ta haife yarinyar da Cecilia ta sayarwa wata mata mai suna Bernadette Chinonso Ihezuo.

NAPTIP ta kama Cecilia Onyema, dillaliyar jarirai a unguwar Sabongari
NAPTIP ta kama Cecilia Onyema, dillaliyar jarirai a unguwar Sabongari
Asali: Facebook

Binciken NAPTIP ya gano cewa Cecelia ta sayarwa da Bernadette, ma'aikaciya a ma'aikatar kudi ta tarayya, jaririn da matashiyar ta haifa a kan farashin kudi N1.5m.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Abinda Magidanci ya fada bayan an kamashi yana lalata 'yar shekara 4 a Masallaci

Sauran ma su laifin da NAPTIP ta kama bayan Cecilia sun hada da uwargida Okasi Ekeoma; 'yar uwa wurin Cecelia, Harrieth Nmezi; mahaifiyar matashiya mai shekaru 16, da kuma Bernadette.

"Dukkan wadanda aka kama sun amsa laifinsu kuma kwanan nan zamu gurfanar dasu a gaban kotu domin a yanke musu hukuncin saba dokokin safarar mutane da aka kirkira a shekarar 2015," a cewarta.

Julie ta jaddada tare da yin gargadin cewa NAPTIP ba zata yarda da duk wata halayya da za ta mayar da yara tamkar wata haja da za a sayar a kasuwa ga duk wani mai kudi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel