Shekara da shekaru: Yadda farashin man fetur ya dunga hauhawa tun daga 2016 zuwa 2020

Shekara da shekaru: Yadda farashin man fetur ya dunga hauhawa tun daga 2016 zuwa 2020

Tun a shekarar 2016, farashin man fetur ke ta yashe aljihun ‘yan Najeriya, yana ta hawa. Kuma babu alamun zai sauka.

A watan Mayun 2016, farashin litar man fetur ya karu zuwa N145 kowani lita, daga N86.50 inda gwamnatin baya ta Goodluck Jonathan ta bar shi.

A watan Maris 2020, an rage farashin man fetur zuwa N125 daga N145.

A watan Mayun 2929, hukumar kula da farashin man fetur (PPPRA) ta sanar da sabon farashin famfon mai tsakanin N121.50 zuwa N123.50 kowani lita.

Ya ci gaba da kasancewa a haka a watan Yuni.

Shekara da shekaru: Yadda farashin man fetur ya dunga hauhawa tun daga 2016 zuwa 2020
Shekara da shekaru: Yadda farashin man fetur ya dunga hauhawa tun daga 2016 zuwa 2020
Asali: UGC

Amma a Yulin 2020, ya kara hawa tsakanin N140.80 da N143.80.

A watan Agustan 2020, ya sake hawa tsakanin N145.86 da N148.86.

Karin baya-bayan nan ya kasance a ranar 2 ga watan Satumban 2020, lokacin da ya kara hawa zuwa N151.56.

Amma yan kasuwa sun bayyana cewa suna iya siyar dashi fiye da haka.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo 2020: Obaseki da Ize Iyamu sun kulla yarjejeniya gaban Sarkin Benin

A baya mun ji cewa farashin man fetur ya karu zuwa N151.1 ga lita, a cewar kamfanin kasuwancin man fetur PPMC, wani sashen kamfanin man feturin Najeriya NNPC.

A takardar da jaridar Vanguard ta bayyana cewa ta samu gani, D.O Abalaka na kamfanin PPMC yace: "Ku sani cewa mun daura sabon farashin mai a shafin rubuta kudi."

"A yanzu, farashin man fetur PMS zai koma naira dari da hamshin da daya, da kwabo hamsin da shida ga lita."

"Za'a fara aiki da sabon farashin daga 2 ga Satumba, 2020."

Har ila yau a wani labarin mun ji cewa am'iyyar All Progressives Congress (APC) ta daura laifin karin farashin man fetur kan jam'iyyar adawa ta PDP da gwamnatocinta na baya.

Jam'iyyar mai ci ta yi raddi ne ga PDP yayin da ta caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara farashin mai da na wutan lantarki yayinda yan Najeriya ke cikin halin talauci.

APC ta ce gwamnatocin PDP da suka shude ne suka sace arzikin kasar nan ta hanyar biyan tallafin mai, kuma hakan ke sabbaba matsalan da ake fuskanta yanzu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel