Buhari ya umarci a fitar da masara ton 30,000 domin samar da abincin kaji

Buhari ya umarci a fitar da masara ton 30,000 domin samar da abincin kaji

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya nuna damuwarsa a kan yadda farshin kayan abinci ya ke hauhawa a kasar nan sannan jama'a na kuka da gwamnatinsa.

mataimaki na musamman ga shugaban kasar a fannin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya sanar da cewa Buhari ya shiga matukar damuwa a kan tsadar kayan abinci a daidai lokacin da kullen korona ya gurgunta tattalin arzikin kasar.

Shugaban ya ce, wannan matsalar ta shafi dukkan duniya kuma gwamnatinsa na kokarin daukar matakin shawo kan matsalar.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, shugaba Buhari ya bada umarnin fitar da abinci kusan ton 30,000 na masara ga masu sana'ar dabbobin kaji a saukakken farashi.

Ya tabbatar da cewa wannan yanayin zai zo ya wuce, ba mai tsayawa bane.

Buhari ya umarci a fitar da masara ton 30,000 domin samar da abincin kaji
Buhari ya umarci a fitar da masara ton 30,000 domin samar da abincin kaji. Hoto daga BBC
Source: UGC

KU KARANTA: Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara ya koma PDP

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya nuna fargabarsa kan yiwuwar yan ta'adda su koma neman mambobi ta hanyar amfani da intanet saboda dokar kulle da aka saka sakamakon korona.

Ya ce saboda haka gwamnati za ta fara sanya idanu a kan ƴan ta'adda a yanar gizo domin kare mutane daga faɗawa tarkonsu.

A cewar sanarwar da kakakinsa, Femi Adesina ya fitar, shugaban ƙasar ya furta hakan ne yayin jawabinsa a taron AQABA da aka yi ta intanet a masarautar Jordan.

An yiwa sanarwar laƙabi da, "A yayin taron intanet ta AQABA, Shugaba Buhari ya yi magana kan alaka tsakanin COVID-19 da tsaro."

Adesina ya ruwaito cewa shugaban ƙasa ya ce komawa amfani da intanet ya haifar da ƙaluballe game da gurɓata tunanin mutane musamman saboda takaita yawo da cudanya.

"Yana da muhimmanci a bayyana cewa yaɗuwar COVID 19 ya saka an koma gudanar da abubuwa ta intanet.

"Kazalika, dokar kulle da taƙaita zirga zirga na nufin mutane za su koma gudanar da harkokinsu a yanar gizo.

"Sai dai hakan ya kawo ƙaruwar hatsarin yiwuwar gurɓata tunanin mutane a yanar gizon," in ji sanarwar.

Amma Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta cigaba da ɗaukan matakai da suka dace da sabon yanayin tare da mayar da hankali kan tsaro a yayin da masana ke kokarin neman riga kafi ko maganin Covid 19.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel