Buhari ya mika ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban jami'ar NOUN, Farfesa Gabriel Ojo

Buhari ya mika ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban jami'ar NOUN, Farfesa Gabriel Ojo

Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyyar sa bisa rasuwar shugaban farko na jami'ar National Open University Noun, NOUN, Farfesa Gabriel Ojo.

Farfesa Ojo ya rasu yana da shekaru 91 a duniya kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Buhari ya yi wa iyalansa, abokansa da abokan aikinsa malaman jami'o'i ta'aziyya cikin saƙon da ya aike a ranar Laraba a Abuja ta hannun kakakinsa Femi Adesina.

Buhari mika ta'aziya ga iyalan tsohon shugaban jami'ar NOUN, Farfesa Gabriel Ojo
Buhari mika ta'aziya ga iyalan tsohon shugaban jami'ar NOUN, Farfesa Gabriel Ojo
Source: Twitter

Shugaban ƙasar ya yi imanin cewa Farfesa wanda ke ɗaya daga cikin malaman da aka kafa jami'ar Obafemi Awolowo da su ya yi rayuwa mai kyau da ya dace ayi koyi da shi.

Ya ce rayuwar marigayin ta nuna cewa duk wanda ya yi haƙuri kuma ya bi abubuwar rayuwa mataki zuwa mataki zai ci nasara a rayuwa.

Farfesan kuma fitaccen marubuci ya samu kyaututuka da lambar yabo da dama daga ƙasashen waje da ma gida Najeriya.

Shugaba kasar ya yi addu'ar Ubangiji ya karbi ran mammacin ya kuma bawa iyalansa hakuri da juriyar rashin sa.

DUBA WANNAN: Akwai yiwuwar ƴan ta'adda za su koma neman mambobi ta hanyar yanar gizo - Buhari

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, Kun ji cewa Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta'aziyya zuwa ga iyali da rundunar soji bisa mutuwar Manjo Janar Samaila Iliya.

A cikin wani jawabi da ya fitar ta bakin kakakinsa, Femi Adesina, Buhari ya bayyana janar Iliya a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa domin hidimtawa kasarsa kafin ya yi ritaya.

Kazalika, shugaba Buhari ya sake mika sakon ta'aziyya ga abokan marigayin, wanda ya bayyana a matsayin wanda ya kasance shugaba abin koyi a lokacin da ya rike mukamai ma su yawa a rudnunar soji.

Buhari ya yi waiwaye a kan irin nasarar da janar Iliya ya samu a lokacin da ya jagoranci tawagar sojojin Najeriya da aka tura domin tabbatar da zaman lafiya a Rwamda da Lebanon.

A cewar Buhari, jarumtar janar Iliya ta sa an nada shi jagorantar tawagar rundunar sojojin kasashen duniya da majalisar dinkin duniya ta tura jamhiriyar Domokradiyyar Kongo (DR Congo) domin tabbatar da zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel