Zakakuran sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga, sun halaka 4 a Kaduna (Hotuna)

Zakakuran sojin Najeriya sun ragargaza 'yan bindiga, sun halaka 4 a Kaduna (Hotuna)

A kokarin ci gaba da tabbatar da zaman lafiya tare da yaki da ta'addanci a kasar nan, zakakuran dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Accord ta lallasa 'yan bindiga a jihar Kaduna.

Dakarun sun kai samame a yankin Jeka Da Rabi da ke babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja,inda suka halaka 'yan bindigar dajin hudu.

Kamar yadda shugaban fannin yada labarai na rundunar, Manjo janar John Enenche, ya bayyana a wata takarda da ya fitar a ranar uku ga watan Satumban 2020, yace, " dakarun sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Accord, sun kai wa 'yan bindiga samame.

"Sun yi nasarar halaka hudu daga ciki a yankin Jeka Da Rabi da ke kan babban titin Abuja zuwa Kaduna."

Ya kara da sanar da cewa, an samu wannan nasarar ne a ranar 2 ga watan Satumban 2020. Dakarun sojin Najeriyan sun yi amfani da bayanan sirrin da suka samu na kaiwa da kawowar 'yan bindigar a yankin Kachia.

"Babu kakkatautwa zakakuran sojin suka yi amfani da bayanan sirrin da suka samu a kan 'yan ta'addan inda suka kai musu samame, " yace.

KU KARANTA: Mun sha matukar azaba - Iyalan Abiola sun bayyana arangamarsu da 'yan bindiga

Rundunar sojin sun yi fito na fito da 'yan bindigair inda suka yi musayawar wuta. A take suka samu nasarar kashe hudu daga ciki yayin da sauran suka tsere da miyagun raunika.

Sun yi nasarar samo bindigogi kirar AK 47 da jigidar harsasai 9.

A halin yanzu dakarun sun ci gaba da mamaye yankin, inda suka tsananta sinitiri domin kokarin cafko 'yan bindigar da suka tsere.

Hukumar rundunar sojin tana farin ciki tare da mika yabo da sam barka ga rundunar a kan jajircewarsu da kwazonsu wanda ya kai ga wannan tarin nasarorin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: