Kano: Yadda aka halaka wani mutum a teburin mai shayi

Kano: Yadda aka halaka wani mutum a teburin mai shayi

- Rundunar 'yan sandan jihar kano ta damke wani mutum da ake zargi da kashe abokin muhawararsa a teburin mai shayi

- Wannan mummunan lamarin dai ya faru ne a kwatas ta Aisami da ke karamar hukumar gwale ta birnin Kano

- An gano cewa, wanda ake zargin ya yi amfani da karfe wurin soka wa abokin muhawararsa wanda hakan ya yi ajalinsa

Wani mutum mai suna Umar Abubakar ya sheka lahira sakamakon rikicin da ya barke a teburin mai shayi, wanda ya ja aka kashe shi har lahira.

Lamarin ya faru a wani teburin mai shayi da ke kwatas ta Aisami a karamar hukumar Gwale da ke tsakiyar birnin Kano.

An gano cewa, an soki mamacin da karfe ne wanda a take yayi ajalinsa. Amma kuma, Auwal Balarrabe, wanda ake zargin da yin aika-aikar ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar.

Kakakin rundunar 'ya sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin.

Ya ce an kwashi Umar Abubakar rai a hannnun Allah zuwa asibitin kwararru na Muratala Muhammad, inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Kiyawa ya ce kwamishinan 'yan sanda na jihar ya bada umarnin bincike mai tsauri a kan lamarin kafin a mika wanda ake zargin gaban kotu.

Kano: Yadda aka halaka wani mutum a teburin mai shayi
Kano: Yadda aka halaka wani mutum a teburin mai shayi. Hoto daga The Nation
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Uwar saurayi da kannansa sun tilasta budurwar wanke kwalliyarta daga zuwa gaisuwa

A wani labari na daban, an kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne a lokacin da ƴan banga a ƙauyen Yantara da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina suka yi fito na fito da ƴan bindiga da suka kai hari ƙauyen ranar Talata.

Wani mutum mai suna Mamman Dahiru mai shekaru 30 a duniya shima ya rasa ransa sakamakon harin.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Laraba.

An gano cewa ƴan bindigan sun kai farmaki ƙauyen ne a misalin ƙarfe ɗaya na daren ranar Talata.

The Punch ta ruwaito cewa sun yi wa mutane rauni, sun yi fashi a gidaje sannan sun sace dabbobi.

Ƴan bangar sun yi wa ƴan bindigan kwantar ɓauna ne suka faɗa musu a hakan ne mutum biyu suka rasa rayukansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel