Bidiyo: Yadda giwa ta kaiwa wani mutumi da yake tafiya a keke hari ta kwace keken shi

Bidiyo: Yadda giwa ta kaiwa wani mutumi da yake tafiya a keke hari ta kwace keken shi

- Wata giwa ta kaiwa wani mutumi da yake tafiya akan keke hari

- Ta kwace keken ta tsaya a kanshi tana kokarin murkushe shi

- Sai dai daga baya mutumin ya samu damar guduwa, inda ita kuma giwar ta dauki keken ta jefar dashi a gefe

Wani bidiyo da yake ta yawo, ya nuna lokacin da wata katuwar giwa ta kaiwa wani mutumi da yake tafiya akan keke hari, ta kayar da shi sannan ta kwace keken.

A bidiyon, mutumin dake tuka keken an ganshi kwance a kasa kusa da keken nashi, yayin da ita kuma giwar ta tsaya a kanshi.

Bidiyo: Yadda giwa ta kaiwa wani mutumi da yake tafiya a keke hari ta kwace keken shi
Bidiyo: Yadda giwa ta kaiwa wani mutumi da yake tafiya a keke hari ta kwace keken shi
Source: Facebook

Mutumin wanda alamu na nuni da cewa ya tsorata. bai gudu ba, maimakon haka sai ya kwanta a wajen.

Mutanen da suka dauki wannan bidiyo suma alamu na nuni da cewa suna tsoron zuwa wajen su taimakawa mutumin. Daga nesa dai an jiyo suna korar giwar ta hanyar yi mata tsawa cikin wani yare.

A wani bangaren, giwar ta dauki keken mutumin ta jefar dashi, sannan ta tsaya akan mutumin tana jiran yayi wani abu ta murkushe shi da kafarta.

KU KARANTA: Tashin hankali: 'Yan ruwa sun kashe budurwa a lokacin da ake yi mata wankan shiga addinin Kirista

Mutanen dake kallon sunyi ta rokar giwar akan tayi hakuri ta tafi.

Haka kuma suna yiwa mutumin magana akan ya gudu, aikuwa a karshe da ya samu hanya sai ya yanka da gudu.

Ba a bayyana ko a wacce kasa ne wannan lamari ya faru ba.

Ga dai bidiyon yadda lamarin ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel