PDP ce ta jefamu cikin wannan halin - APC ga yan Najeriya kan karin farashin mai da wuta

PDP ce ta jefamu cikin wannan halin - APC ga yan Najeriya kan karin farashin mai da wuta

- Jam'iyyar APC ta yi tsokaci kan karin farashin man fetur a gwamnati tayi

- Jam'iyyar ta daura laifin hakan kan gwamnatocin PDP da suka shude

- Ta na martani ne ga jam'iyyar PDP da ta caccaki shugaba Buhari kan tsananta rayuwan yan Najeriya

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta daura laifin karin farashin man fetur kan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da gwamnatocinta na baya.

Jam'iyyar mai ci ta yi raddi ne ga PDP yayindata t a caccaki gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara farashin mai da na wutan lantarki yayinda yan Najeriya ke cikin halin talauci.

APC ta ce gwamnatocin PDP da suka shude ne suka sace arzikin kasar nan ta hanyar biyan tallafin mai, kuma hakan ke sabbaba matsalan da ake fuskanta yanzu.

Kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena, ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Wani sashen jawabinsa yace: "Muna kira ga PDP ta baiwa yan Najeriya mamaki ta hanyar yiwa shugabanninsu magana (yawancinsu dake kasashen waje) da suka sace mana arziki ta hanyar biyan tallafin mai, su dawo mana da su."

"Karkashin shugaba Muhammadu Buhari, an daina samun karancin man fetur da layukan motoci."

PDP ce ta jefamu cikin wannan halin - APC ga yan Najeriya kan karin farashin mai da wuta
PDP ce ta jefamu cikin wannan halin - APC ga yan Najeriya kan karin farashin mai da wuta
Source: UGC

Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa Farashin man fetur ya karu zuwa N151.1 ga lita, a cewar kamfanin kasuwancin man fetur PPMC, wani sashen kamfanin man feturin Najeriya NNPC.

A takardar da jaridar Vanguard ta bayyana cewa ta samu gani, D.O Abalaka na kamfanin PPMC yace: "Ku sani cewa mun daura sabon farashin mai a shafin rubuta kudi."

"A yanzu, farashin man fetur PMS zai koma naira dari da hamshin da daya, da kwabo hamsin da shida ga lita."

"Za'a fara aiki da sabon farashin daga 2 ga Satumba, 2020."

Hakan ya sa marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya suka bayyana rashin amincewarsu da karin farashin litan man fetur.

Yan majalisan, a jawabin da shugabansu, Hanarabul Ndudi Elumelu yayi, ya cewa ba zasu taba amincewa da wannan kari ba saboda zai sabbaba hauhawar kayan masarufi da abubuwa kuma zai tsananta halin kuncin da yan Najeriya ke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel