FCTA ta dawo da tsarin rusau na mako - mako a Abuja

FCTA ta dawo da tsarin rusau na mako - mako a Abuja

Hukumar kula da birnin tarayya (FCTA) ta alakanta yawaitar gine-gine ba bisa ka'ida ba a Abuja da bullar annobar korona.

FCTA ta sanar da cewa za ta dawo da tsarin fita aiki na mako-mako domin rushe irin wadannan wurare da aka gina ko aka kafasu a cikin Abuja ba bisa ka'ida da tsari ko samun izinin gwamnati ba.

Darekta a FCTA, Mukhtar Galadima, ne ya sanar da hakan yayin da ya kai ziyarar aiki a sassan birnin Abuja da suka hada da Guzape, Asokoro, Katampe, da rukunin gidjen 'yan majalisu na unguwar Apo.

A cewarsa, wasu mutane sun yi amfani da dakatar da aiyuka da aka yi sakamakon bullar annobar korona wajen yin saurin gina filaye ba tare da izinin hukuma ko bin ka'ida da tsari ba.

"Zan iya alakanta abinda na gani da bullar annobar korona, saboda duk yawancin gine-ginen an yi su ne lokacin da aka saka dokar kulle," kamar yadda ya bayyana.

FCTA ta dawo da tsarin rusau na mako - mako a Abuja
FCTA ta dawo da tsarin rusau na mako - mako a Abuja
Source: Facebook

Ya ce hukuma za ta dauki matakin da ya dace a kan kowanne gini, tare da bayyana cewa akwai wadanda za a ci tararsu, akwai kuma wadanda ya zama dole a rushe gininsu.

Tawagar ta ma'aikatan FCTA da Galadima ke jagoranta ta ziyarci wasu gine-gine da aka sakawa alamar rusau a unguwar Guzape, Asokoro, Katampe da Apo.

DUBA WANNAN: Yadda zamu narka biliyan N600 a bangaren noma - Minista Sabo Nanono

Da ya ke magana a kan wani gini da za a rushe a yankin Guzape, Galadima ya nuna bacin rai da mamakinsa a kan yadda kamfanin da ke aiki a wurin ya saba yarjejeniyar da aka kulla tsakaninsa da gwamnati.

Galadima ya ce kamfanin ya zarce ka'ida ta hanyar gina rukunin gidaje takwas sabanin hudu da hukuma ta bashi izinin ginawa, kuma gashi har sun kusa kammala aikin ginin.

"Mun je unguwar Asokoro ne saboda abinda da ya taba faruwa a baya, inda wani mutum ya yi kokarin gina otal bayan hukuma ta bashi izinin gina gidan zama, shi yasa ba zamu yi sake da rangadi a unguwar ba," a cewarsa.

Galadima ya ce sun ware ranar Talata ta kowanne mako domin fita rangadin unguwannin Abuja domin zakulo irin wadannan gine-gine tare da daukan mataki a kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a:

Source: Legit Nigeria

Online view pixel