Mun sha matukar azaba - Iyalan Abiola sun bayyana arangamarsu da 'yan bindiga

Mun sha matukar azaba - Iyalan Abiola sun bayyana arangamarsu da 'yan bindiga

Iyalan marigayi Moshood Abiola, wanda ya ci zaben ranar 12 ga watan Yunin 1993 na shugaban kasa a Najeriya, sun bayyana arangamarsu da 'yan bindiga.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kutsa gidan marigayin fitaccen dan kasuwar da ke Ikeja a jihar Legas a ranar Laraba.

A wata takardar da aka fitar a madadin iyalan, Tundun Abiola, diyar marigayin dan kasuwar ta ce, tuni suka sanar da 'yan sanda kuma an fara bincikar lamarin.

Ta ce 'yan bindigar sun matukar azabtar da iyalan tare da hantararsu. Tundun ta kara da cewa, barayin sun kwashe kudi da wasu kadarori daga gidan bayan kutsawarsu.

"'Yan bindigar sun gallazawa iyallan tare da hantararsu inda suka kwashe kudi da wasu kadarori a gidan," takardar tace.

"Tuni muka sanar da 'yan sanda. Ana bincikar aukuwar lamarin. Hankalinmu ya kwanta ganin cewa babu rai da aka rasa yayin mummunan lamarin.

"Muna godiya ga Allah kuma muna mika godiyarmu ga 'yan uwa da abokan arziki a fadin duniya da suka kira tare da turo mana sakonnin jaje," tace.

Mun sha matukar azaba - Iyalan Abiola sun bayyana arangamarsu da 'yan bindiga
Mun sha matukar azaba - Iyalan Abiola sun bayyana arangamarsu da 'yan bindiga. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Makasan maza: Yadda matasa suka bi 'yan bindiga, suka kashe 1 tare da kwato shanunsu

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Bala Elkana, ya sanar da jaridar The Cable cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargin suna da hannu a cikin lamarin.

"Wasu wadanda ake zargi sun shiga hannunmu kuma mun fara bincike," yace.

Abiola ya ci zaben shugabancin kasa da aka yi a Najeriya a shekarar 1993, wanda gwamnatin mulkin soji karkashin shugabancin Ibrahim Babangida ta soke.

A 2018, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya amince da mayar da ranar damokaradiyya ta kasar nan zuwa ranar 12 ga watan Yuni don karrama Abiola, wanda ya karrama shi a kasar nan duk da bashi da rai

Legit.ng ta ruwaito cewa, wasu mutane dauke da bindigu da har yanzu ba a san ko su wanene ba sun afka gidan Moshood Abiola da ke Ikeja a Legas.

fashin sun sace kudade masu yawa na ƙasashe daban-daban da a halin yanzu ba a tabbatar da adadin su ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel