Buhari ya ware ranar 1 ga watan Nuwamba ta kowacce shekara a matsayin ranar matasa

Buhari ya ware ranar 1 ga watan Nuwamba ta kowacce shekara a matsayin ranar matasa

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da ayyana ranar 1 ga watan Nuwamba ta kowacce shekara a matsayin ranar matasa ta ƙasa.

An ware ranar ne domin taya matasan murna, janyo hankulan mutane a kan batutuwan da suka shafi matasan da gano hanyoyin warware su.

Buhari ya ayyana ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar matasa
Buhari ya ayyana ranar 1 ga watan Nuwamba a matsayin ranar matasa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

Ministan Matasa da Cigaban Wasanni, Sunday Dare ne ya sanar da hakan a shafin Twitter jim kadan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa na Ƙasa.

Ga abinda Mista Dare ya wallafa: "A yau, yayin taron majalisa, Buhari ya amince da ware duk ranar 1 ga watan Nuwambar kowacce shekara don taya matasa murna, janyo hankula kan batutuwan da suka shafe su tare da warware su. Shugaban ƙasa ya sake nuna himmar gwamnatinsa wurin tallafawa tsare tsare da za su amfani matasa. Na gode."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164