COVID-19: Ya kamata Buhari ya rika amfani da takunkumi inji Anthony Sani

COVID-19: Ya kamata Buhari ya rika amfani da takunkumi inji Anthony Sani

- Anthony Sani ya yi magana game da yaduwar COVID-19 a Najeriya

- Sani ya na cikin manyan shugabannin kungiyar dattawa na Arewa

- A cewarsa, sai shugabanni sun bi doka idan ana so a yaki Coronavirus

Tsohon sakataren kungiyar Arewa Consultative Forum ta dattawan Arewa, Anthony Sani, ya yi kira ga shugabanni su rika bin dokokin yaki da COVID-19.

Mista Anthony Sani ya ce hanyar da za a yaki da Coronavirus ita ce shugaban kasa, gwamnoni da sarakunan gargajiya duk su rika amfani da takunkumin fuska.

Ta hakane Sani ya ke ganin za a dakile yaduwar annobar COVID-19, a kuma kare yaduwar wannan cuta, wanda wannan zai yi sanadiyyar kare rai.

Jigon na kungiyar dattawan ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya aikawa jaridar Punch a Kaduna.

A cewar Sani, babu dabarar da ta ragewa Najeriya sai a koma garkame fuska domin a gujewa kamuwa da wannan cuta ta murar mashako.

KU KARANTA: DSS sun gargadi Tiwa Savage da Don Jazzy a kan sukar Buhari

COVID-19: Ya kamata Buhari ya rika amfani da takunkumi inji Anthony Sani
Buhari dauke da takunkumin fuska a Mali
Source: UGC

“Ganin yadda ake samun raguwar masu dauke da cutar COVID-19 a Najeriya, la’akari da rashin magani a yanzu, kuma mun gaza bin dokokin gujewa shiga cunkoso, abin da ya ragewa Najeriya shi ne kawai kowa ya rika rufe fuska.”

Ya ce: “Hanyar da za a tilasta bin doka ita ce shugaban kasa Muhammadu Buhari, duka gwamnoni, da sarakunan gargajiya su zama abin koyi, su rika amfani da takunkumin fuska.”

Anthony Sani ya ce kowa ya tabbatar ya rufe fuskarsa idan ya shiga bainar jama’a kamar kasuwanni, wuraren ibada da kuma tashoshin mota.

“Ta haka za a takaita yaduwar cutar domin dakile annobar, da kuma kare rayukan al’umma, tsare asibitoci, sannan a bunkasa tattalin arziki.” Inji Sani.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel