An yiwa wasu yara guda 2 kyautar naira miliyan 43, bayan an iske su suna aikin makaranta a wajen sayar da abinci

An yiwa wasu yara guda 2 kyautar naira miliyan 43, bayan an iske su suna aikin makaranta a wajen sayar da abinci

- Wani hoto na wasu yara guda biyu dake yawo a shafukan sadarwa suna aikin makaranta a gaban wani wajen cin abinci ya taba zuciyar mutane da dama

- Iyayen yaran baza su iya biyan kudin data ba, hakan ya sanya suka fito bakin wannan wajen cin abinci domin yin amfani da WiFi na wajen.

- Mutane da yawa da suka nuna tausayawarsu ga wadannan yara sun nuna kokarinsu na taimakawa, inda suka bude wani shafi na neman taimako

Wasu 'yan gudun hijira a birnin California sun samu tallafi daga wajen mutane da dama bayan an wallafa hotunan wasu yara kanana guda biyu da suke amfani da WiFi na wajen sayar da abinci domin gabatar da aikin makarantarsu.

Hoton da aka wallafa kimanin mako guda da ya wuce a shafukan sadarwa, ya nuna jajircewa ta yaran da suka fito daga gidan da basu da hali, inda suka dage wajen karatu duk da wannan yanayi da ake ciki na coronavirus.

An yiwa wasu yara guda 2 kyautar naira miliyan 43, bayan an iske su suna aikin makaranta a wajen sayar da abinci
An yiwa wasu yara guda 2 kyautar naira miliyan 43, bayan an iske su suna aikin makaranta a wajen sayar da abinci
Source: UGC

A rahoton da NBC News ta fitar, yaran dalibai ne na Salinas City Elementar, wacce tace tayi kokarin bayar da intanet ga iyalan wadannan yara.

Sai dai kuma wadanda suka ga wannan hotuna na yaran, sun nuna rashin jin dadinsu akan wadannan yaran, inda suka yi kokarin taimakawa wajen kawo karshen halin da suke ciki.

Hakan ya sanya suka bude shafin yanar gizo, suka sanya mishi suna GoFundMe, inda wata mai suna Jackie Lopez, wacce ta samu damar magana da iyayen yaran ta bude.

KU KARANTA: Shekarata 20 ina aikin N700 a rana, amma hakan yafi mini rufin asiri da naje nayi sata - Cewar Lebura

A cewar NBC, Lopez ta gano cewa ana shirin korar iyayen yaran daga karamin gidan da suke zaune a ranar Litinin din data gabata 31 ga watan Agusta, shafin da suka bude ya samu nasarar tara har naira miliyan 43.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel