Buhari ya jajanta, ya fadi illar da ambaliyar ruwa a Kebbi zata yi wa kasa

Buhari ya jajanta, ya fadi illar da ambaliyar ruwa a Kebbi zata yi wa kasa

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fitar da sakon jaje ga jama'ar jihar Kebbi a kan asarar rayuka da amfanin gona da ambaliyar ruwa ta haifar a jihar.

Da ya ke mika sakon ta'aziyya ga wadanda su ka rasa wasu nasu sakamakon ambaliyar, Buhari ya bayyana cewa asarar kayan amfanin gona za ta shafi wadatuwar kayan abincin da ake nomawa a gida Najeriya.

Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya fitar ta hannun babban kakakinsa, Malam Garba Shehu.

"Shugaba Buhari ya jajantawa jama'ar jihar Kebbi da ambaliyar ruwa ta halaka 'yan uwansu tare da lalata musu gonakinsu.

"Wannan ambaliya ba kankanin koma baya za ta haifarwa Najeriya ba ta fuskar abincin da ake nomawa a cikin kasa, za ta kawo nakasu ga kokarin gwamnati na ganin an samu wadatuwar kayan abinci, musamman shinkafa.

"Ambaliyar za ta kawo cikas a kokarin gwamnati na hana shigo da shinkafa daga kasashen ketare.

Buhari ya jajanta, ya fadi illar da ambaliyar ruwa a Kebbi zata yi wa kasa
Buhari da Bagudu
Asali: UGC

"Jihar Kebbi ta na daga cikin jihohin da wannan gwamnati ta dogara da su domin cimma manufarta na noma shinkafar da za ta wadata Najeriya," a cewar wani bangare na jawabin shugaba Buhari.

DUBA WANNAN: Subhanallah: Jaridar Charlie Hebdo ta sake buga hotunan batanci ga Annabi Muhammadu

Ambaliyar ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 6 tare da lalata gonakin dumbin manoma a jihar Kebbi.

An yi kiyasin cewa ambaliyar ruwan ta lalata amfanin gona na biliyoyin Naira.

Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta hada kai da gwamnatin Kebbi domin ganin cewa an tallafawa manoman da ambaliyar ruwan ta yi wa barnar amfanin da suka shuka gonakinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng