Ku mayar da makaman da kuka kwace hannun jami'an tsaro - Gwamna ya gargadi yan ta'addan IPOB

Ku mayar da makaman da kuka kwace hannun jami'an tsaro - Gwamna ya gargadi yan ta'addan IPOB

Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwanyi, ya yi kira ga mambobin kungiyar masu rajin kafa kasar Biyafara IPOB, su mayar da makaman da suka kwace daga hannun jami'an yan sanda.

Za ku tuna cewa a ranar 23 ga Agusta, 2020, an yi rikici tsakanin jami'an DSS da matasan IPOB masu zanga-zanga idan hakan yayi sanadiyar mutuwar hafsoshin DSS biyu.

Bayan haka a ranar 28 ga watan, wasu matasa sun kai farmaki ofishin yan sandan tashar jirgin kasa dake Ogui da kuma ranar 30 ga wata a ofishin yan sandan Abapka inda suka kwashe makamai.

Gwamnan ya ce su mayar da makaman da suka kwace wajen sarakunan gargajiyansu saboda a mayarwa hukuma.

Gwamnan ya bayyana hakan ne jiya bayan ganawar gaggawan da yayi da shugabannin hukumomin tsaron a jihar.

Yayin hira da manema labarai bayan zaman da akayi a gidan gwamnatin jihar dake Enugu, Ugwanyi ya bayyana jimaminsa kan rayukan da aka rasa a ranan.

Ku mayar da makaman da kuka kwace hannun jami'an tsaro - Gwamna ya gargadi yan ta'addan IPOB
Enugu
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Buhari ya shiga zaman majalisar zartaswa da ministocinsa

Yace: "Bayan zaman majalisar tsaro da mukayi....ya zama wajibi mu baiwa wadanda ke da hakkin bincike kan lamarin lokaci su kammala aikinsu."

"Abinda ya faru ranar 23 ga Agusta, 2020, da yayi sanadiyar mutuwan mambobin hukumar DSS da yan jihar Enugu da kuma harin da aka kai ofishin yan sandan jirgin kasa a ranar 28 ga Agusta, 2020 da ofishin yan sandan Abakpa a ranar 30 ga Agusta, 2020, inda aka kwashe makamai, abin damuwa ne gare ni."

Yayinda yake kira ga al'ummar jihar su kasance cikin zaman lafiya da fahimta "yayinda ake aiki tare domin tabbatar da zaman lafiyan da aka dade ana jin dadi a jihar Enugu," gwamnan ya bayyana cewa majalisar tsaron jihar ta amince da sabon sintirin hadakar dukkan jami'an tsaro.

Hakazalika za'a zauna da shugabannin gargajiya. malaman addini da masu ruwa da tsaki ranar alhamis, 3 ga Satumba, 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel