Zaben 2023: An bayyana dan siyasar da zai gaji shugaba Buhari a Najeriya

Zaben 2023: An bayyana dan siyasar da zai gaji shugaba Buhari a Najeriya

- An sako Orji Uzo Kalu a gaba akan maganar da yayi kan shugabancin kasa a 2023

- Tsohon gwamnan Abia din, a wata ziyara da ya kaiwa Janar Ibrahim Babangida, ya bayyana cewa babu bangaranci a jam'iyyar APC

- A wani martani da SEFORP2023 tayi ta caccaki Kalu akan bayyana gaskiya kan cewa shugabanci zai koma Kudu ne bayan shugaba Buhari ya kammala aiki

An caccaki Sanata Orji Uzor Kalu, kan maganar da yayi ta takarar shugabancin kasa a shekarar 2023, inda aka jiyo shi yana cewa babu bangaranci a jam'iyyar APC.

Wata kungiya ce ta kamfen din shugaban kasa a 2023 dake kudancin Najeriya mai suna (SEFORP2023) ta caccaki tsohon gwamnan.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 1 ga watan Satumba, dan majalisar dole ya fuskanci gaskiya ya cire zancen cewa babu bangaranci a zaben shugaban kasar a 2023.

Zaben 2023: An bayyana dan siyasar da zai gaji shugaba Buhari a Najeriya
Zaben 2023: An bayyana dan siyasar da zai gaji shugaba Buhari a Najeriya
Asali: UGC

Legit.ng ta gano cewa Kalu ya je garin Minna dake jihar Neja, a ranar 31 ga watan Agusta, a wata ziyara da ya kaiwa Janar Ibrahim Babangida da Janar Abdulsalam Abubakar.

A wannan ziyara ne tsohon gwamnan Abia din yayi watsi da zargin cewa akwai rikici a jam'iyyar APC a sakamakon bangaranci da aka yi a kujerar shugaban kasa a 2023.

Amma a nata martanin, SEFORP2023, ta bakin babban jami'inta, Okechukwu Obiaha, ta nuna rashin jin dadinta akan abinda Kalu ya ce na cewa kowa na da ikon fitowa takara a shekarar 2023 a jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Dangote ya bukaci a bawa Okonjo Iweala babban mukami a WTO

"SEFORP2023 bata ji dadin jin magana irin wannan ta fito daga bakin wanda yake wakiltar mutanen Kudu maso Gabas ba, a matsayin shi na Sanata. Wannan abin kunya da yawa yake.

"Muna shawartar shi ya canja matsayin shi akan wannan magana da yayi, ya sani cewa kujerar na Arewa ne a yanzu, kuma za ta dawo Kudu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel