Tashin hankali: 'Yan ruwa sun kashe budurwa a lokacin da ake yi mata wankan shiga addinin Kirista

Tashin hankali: 'Yan ruwa sun kashe budurwa a lokacin da ake yi mata wankan shiga addinin Kirista

Wata mata mai shekaru 26 da aka bayyana sunanta da Rutendo Nhemachena an ruwaito cewa ta mutu a yayin da ake yi mata wankan tsarki na shiga addinin Kirista a kogin Manyame dake Zimbabwe

An bayyana cewa aljanun ruwane suka shiga jikin Rutendo, inda ta haukace ta fada tsakiyar ruwan inda Fasto Isaac Manyemba yake yiwa wasu maza da mata wanka, da mataimakiyar shi mai suna Madzimai Jennifer.

HMetro ta ruwaito cewa mutanen dake tare da ita sun gano cewa aljannun ruwan sun jata cikin ruwan da karfin tsiya, su kuma basu yi kokarin ceto ta ba. Manyemba ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace Nhemachena tafi karfin shi, kuma ya tabbatar aljanun ruwa ne suka shiga jikinta.

Tashin hankali: 'Yan ruwa sun kashe budurwa a lokacin da ake yi mata wankan shiga addinin Kirista
Tashin hankali: 'Yan ruwa sun kashe budurwa a lokacin da ake yi mata wankan shiga addinin Kirista
Source: Facebook

Faston ya ce:

"Sun roke ni, ni kuma na kai su bakin kogin da muke yiwa mutane maza da mata wankan tsarki, a lokacin ne aljanun suka shiga jikin Nhemachena.

"Ta tura mu duka cikin ruwan, munyi kokarin riketa amma muka kasa, daga baya muka nemeta muka rasa.

"Mun ci karo da wata mata da ta bayyana mana cewa ita ma 'yan ruwa sun taba dauke mata danta lokacin da yana shekara 7, amma sun dawo mata da shi a lokacin da ya cika shekara 14.

Wata mata da tayi magana da yawun 'yan uwan Nhemachena mai suna Patience Gwebede, ta karyata zargin cewa 'yan ruwa ne suka tafi da ita. Ta ce za a binne marigayiyar a Chihota, bayan an gano ta.

KU KARANTA: Tashin hankali: Yadda aka zaro wani maciji mai tsawon gaske daga cikin wata mata, bayan ya shiga ta bakinta lokacin da take bacci

Ta ce:

"Muna bukatar ayi hukunci, sannan kuma muna bukatar ayi mana bayani gamsasshe daga bakin Madzibaba da kuma Madzimai, wadanda suke yiwa mutane wankan."

Kakakin rundunar 'yan sanda AC Paul Nyathi ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace 'yan sanda suna cigaba da bincike akan lamarin wanda yayi sanadiyyar mutuwar ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel