Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya

Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya naɗa Ibrahim Ibrahim a matsayin mataimakinsa na musamman bayan ceto shi daga gidan yari a Saudiyya.

An tsare shi ne na kimanin shekaru uku kan zarginsa da safarar miyagun kwayoyi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa an tsare Ibrahim ne a shekarar 2017 a Saudiyya yayin da ya tafi umara kan wata jaka da ake zargin miyagun kwayoyi ke ciki.

Bayan kwashe shekaru uku ana shari'a, Ibrahim ya samu ƴanci sakamakon daukan lauyoyi da Gwamna Matawalle na Zamfara ya yi Attoney Janar na Najeriya.

Da ya ke sanar da nadin a ranar Talata, Kakakin gwamnan, Zailani Bappa cikin wata sanarwa ya ce Matawalle ya tarbi malamin a gidan gwamnati jim kedan bayan isarsa ƙasar.

A cewar Bappa, "Anyi haduwa mai sosa zuciya a yayin da Gwamnan ya mika malamin ga iyalansa da suka yi shekaru kusan hudu suna kewansa yayin da ya ke gidan yari yana jirar hukuncin kisa."

"Gwamnan bayan sanar da naɗin Hafeez Ibrahim a matsayin mataimakinsa na musamman ya ce gwamnati za ta cigaba da gwagwarmayar ƙwato hakkin duk wani ɗan jihar duk inda ya ke.

"Ya ce abinda ya faru da Hafeez darasi ne ga dukkan masu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje su rika saka idanu a kan jakunkunansu," a cewar sanarwar.

Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya
Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Kudancin Kaduna: Mabiya sun ce fasto ya siyo bindigu da kudin baikonsu

A wani labari na daban, wani Malamin Islamiyya mai suna, Isma'ila Saheed, mai shekaru 38 ya shiga hannu tare da wani mai suna Toliha Sabith, mai shekaru 20, sakamakon kama su da jami'an rundunar' yan sandan jihar Ogun suka yi da laifin yiwa yarinya 'yar shekara 15 fyade.

A wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya fitar, ya ce an kama masu laifin ne a cikin karshen makon nan, bayan wacce aka yiwa fyaden ta kai karar cewa sun yi mata fyade a ranar 23 ga watan Agusta.

A yadda rahotannin suka bayyana, yarinyar tace Sabith ne ya fara yi mata fyade a Imedu-nla dake Mowe, sai taje ta kai karar mutumin wajen Malaminta na Islamiyya, shi ma sai yayi amfani da wannan damar ya biya bukatar shi, ta hanyar ce mata zai taimaka mata ya cire mata cikin da mutumin farkon yayi mata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel