Zaman lafiya zai kare idan aka fitar da sunayen ƴan kwangilar NDDC - Cairo

Zaman lafiya zai kare idan aka fitar da sunayen ƴan kwangilar NDDC - Cairo

Babban daraktan kwangiloli na hukumar ci gaban Neja Delta (NDDC), Cairo Ojougboh, ya ce Najeriya zata tarwatse idan har hukumar ta saki jerin sunayen manyan ‘yan Najeriya da suka amfana daga ayyukan kwangiloli da hukumar ta bayar.

Kallo ya koma kan hukumar NDDC bayan majalisar dokokin tarayya ta kaddamar da bincike kan zargin badakalar kudade a hukumar.

Binciken ya dauki sabon salo lokacin da ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya zargi ýan majalisar tarayya da daukar babban kaso a kwangilolin da hukumar ta rabar.

Har da Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan NDDC, cikin wadanda ministan ya ce sun amfana da kwangilolin.

Sauran sune Peter Nwaoboshi, Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan asusu, Matthew Urhoghide da sanata mai wakiltan Delta ta Kudu, James Manager.

Zaman lafiya zai kare idan aka fitar da sunayen ƴan kwangilar NDDC - Cairo
Zaman lafiya zai kare idan aka fitar da sunayen ƴan kwangilar NDDC - Cairo Hoto: Nigerian Monitor
Asali: UGC

Majalisar dokokin tarayyar ta kuma karyata zargin cewa mambobinta sun amfana daga kwangilolin da hukumar ta bayar.

A wata hira da jaridar Vanguard, Ojougboh ya ce Nwaoboshi da Olubunmi Tunji-Ojo, Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan NDDC, da sauran majalisar dokokin tarayya na da hannu a cikin badakalar kwangilolin.

Ya ce Najeriya zata tarwatse idan aka saki cikakken sunayen wadanda suka amfana da kwangilolin.

“Majalisar dokokin tarayya na da hannu a ciki. A karshen binciken kudin, za ku ga mambobin majalisar dokoki. Wani sanata ya fito ya bayyana cewa a cikin jerin sunaye na 2016 da suka kawo, cewa kwangiloli shida kawai yake da shi, nace a’a, cewa yana da fiye da hakan. Abunda bai sani ba shine bamu saki sunayen na 2017 ba da na 2019. Idan muka sake shi kasar nan za ta tarwatse.

“Oh, saboda mutanen da ke sata, rukunin mutanen, sunaye da mutanen da ke sata a NDDC. Kuma su wanene injiniyoyin? Shugabannin NDDC a majalisar dattawa da majalisar wakilai a majalisar dokokin tarayya.” In ji shi.

Ojougboh ya ce naira miliyan 51 da mukaddashin daraktan hukumar ya kashe ya kasance na tsaronsu.

KU KARANTA KUMA: Rikici ya barke a kotu, yayin da miji yace ya fasa sakin matarshi bayan Alkali ya riga ya raba auren

“MD dina yana ciyar da jami’an yan sanda 100 a kullun a Port Harcourt a matsayinsa na Shugaban NDDC, yana bukatar tsaro fiye da komai, har gobe, kun san da batun. A lokacin da suke tura wadannan jami’an yan sanda, umurnin shine a ciyar dasu, a kula da su, wannan shine a wasikar da hukumar yan sandan ta aiko,” in ji shi.

“Don haka mutane na maganar kimanin naira miliyan 51 na MD, na tsaro ne, ba wai aljihunsa ya tafi ba, kudin baya tafiya asusun MD.

“Ni kaina, naira miliyan 18, bai shiga asusuna ba, yana yafiya ne ga bangaren tsaro da sauran abubuwa, babu damfara a ciki.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel