Rikici ya barke a wajen biki, bayan 'yan uwan miji sun gano cewa amaryar da zai aura tana da miji

Rikici ya barke a wajen biki, bayan 'yan uwan miji sun gano cewa amaryar da zai aura tana da miji

An samu hatsaniya a ranar Asabar a wata coci dake kan hanyar Ako Aro, a yankin Ifako-Ijaiye dake jihar Legas, bayan Iberemu Osadebe, ya kawo karshen bikin da ake yi a coci

Ya bayyana cewa amaryar da ake aurenta matarsa ce.

PUNCH ta gano cewa Osadebe yayi auren gargajiya da Gloria bayan sun haifi yaro tare.

Sai dai daga baya ya kamu da rashin lafiya tsawon shekara biyar ana fama, inda har ya sayar da duka kadarorinsa wajen neman magani.

Mutumin wanda yake dan asalin jihar Imo ya tafi mahaifarsa a Isiala Mbano, inda ya cigaba da jinya a can.

Wakilin PUNCH ya gano cewa, yana kwance cikin rashin lafiya ya samu labarin cewa matar shi da suka yi aure tare shekara 20 za ta auri wani mutumi a ranar Asabar 29 ga watan Agusta.

Rikici ya barke a wajen biki, bayan 'yan uwan miji sun gano cewa amaryar da zai aura tana da miji
Rikici ya barke a wajen biki, bayan 'yan uwan miji sun gano cewa amaryar da zai aura tana da miji
Source: Facebook

Sakamakon haka ya sanya jinin shi ya hau, har yasa ya kasa yin magana.

Ya dawo Legas ranar Juma'a, kwana daya saura daurin auren, ya bayyana shirinsa na kawo cikas wajen daurin auren.

A lokacin da ya isa cocin da misalin 11 na safe, wasu daga cikin shugabannin cocin da suka gane shi sun bukaci yayi hakuri ya manta da maganar.

An gano cewa cocin ta daga bikin, bayan ta gano abinda ke shirin faruwa a cocin.

Faston cocin na shirin daura auren kenan, sai 'yan uwan Osadebe suka isa suka bayyana cewa matar ta jima da yin aure saboda haka ba zai yiwu ayi aure kan aure ba.

Masu gadin cocin sun yi kokarin fitar dasu daga cocin yayin da rikicin ke shirin barkewa.

KU KARANTA: Ciwon zuciya ya kama amarya a daidai lokacin da ake tsaka da bikinta

Osadebe ya ce: "Matata ce tsawon shekaru 20; mun haihu a shekarar 2011. Mahaifiyata bata so auren ba, saboda ita ba 'yar kabilar mu bace, amma nace mata ina sonta.

'Lokacin da mahaifiyata ta mutu naso mu tafi jana'izarta da matata amma taki yadda saboda tace a al'adarsu duk macen da ba'a biya sadakinta ba baza ta iya yin wannan tafiyar ba. Haka kuma ta hanani tafiya da dana.

"Lokacin dana je kauyen mu, manyan garin sunyi fushi dani akan banje da matata da dana ba. Sun ci tara ta N40,000 akan haka, bayan haka nayi alkawarin biyan sadakinta.

"Na sayar da filina naira miliyan daya, na tura mata N500,000 don ta ajiye. A shekarar 2017, muka je wajen danginta muka biya N280,000 a matsayin sadaki. Suka bukaci man gyada, doya da sauransu, duka muka biya N60,000."

Tsohon direban motar, ya ce bayan kamu da rashin lafiya ya koma kauyensu da zama, amma matarsa taki bin shi.

Ya ce a lokacin da bashi da lafiya, matarshi ta kira shi tace mishi basu da kayan abinci, haka ya sanya yace su sayar da motarshi ta biya kudin makarantar dansu.

Osabede ya ce hankalin shi ya tashi a lokacin da ya samu labarin matarshi za ta yi aure.

Ya ce duk da yana son matar shin, amma dole ya sanya ya rabu da ita, amma dole sai ta dawo masa da dansa da kuma sadakin da ya biya.

Daya daga cikin 'yan uwan mijin, Richard Ikere, ya bayyana cewa yana daga cikin mutanen da suka biya sadakin matar a garinsu Uromi, dake yankin Esan ta Arewa maso Gabashin jihar Edo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel