Boko Haram sun kashe Hakimai 13, da wasu manyan masu mukami a jihar Borno - Shehun Borno

Boko Haram sun kashe Hakimai 13, da wasu manyan masu mukami a jihar Borno - Shehun Borno

Shehun Borno, Alhaji Garbai El-Kanemi, ya sanar da cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun kashe kimanin Hakimai 13 da Dagatai masu yawan gaske a jihar Borno, bayan raba dubunnan mutane da suka yi da gidajensu

Shehun Borno, Alhaji Garbai El-Kanemi, ya bayyana cewa an kashe Hakimai 13 da kuma Dagatai da yawan gaske a cikin Masarautarsa, a lokacin da Boko Haram ke cin karenta babu babbaka.

Sarkin ya bayyana haka ne a Maiduguri a wata ziyara da tawagar Sanatoci suka kawo masa, wacce Sanata Abubakar Yusuf, yake jagoranta, domin ganin yanayin aikin da Kwamitin Cigaban Arewa maso Gabas (NEDC) take yi a yankin.

Boko Haram sun kashe Hakimai 13, da wasu manyan masu mukami a jihar Borno - Shehun Borno
Boko Haram sun kashe Hakimai 13, da wasu manyan masu mukami a jihar Borno - Shehun Borno
Asali: Depositphotos

El-Kanemi haka kuma ya bayyana cewa wannan rikici da aka shafe shekaru ana fama yayi sanadiyyar raba dubunnan mutane da gidajensu, inda a yanzu suke zaune a sansanin 'yan gudun hijira daban-daban a fadin jihar.

Ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne a watan Yulin shekarar 2009, bayan matsala da aka samu tsakanin 'Yan Izala da kuma 'Yan Yusufiya.

El-Kanemi ya bayyana cewa rikicin daga baya ya canja salo, inda aka dinga kaiwa 'yan sanda hari, ana kwashe makamai daga ofisoshin su.

KU KARANTA: Bude makarantu: Gwamnatin tarayya ta gargadi jihohin da suke shirin bude makarantu a Najeriya

Ya ce: "A hankali sai suka canja kai hare-harensu daga cikin Maiduguri zuwa kananan hukumomi da kuma wasu garuruwa a cikin Borno. Sakamakon hare-haren da suke kaiwa, masarauta tayi asarar kimanin Hakimai 13 tare da Dagatai da, wadanda duka aka kashe su a masarautunsu.

"Duk wannan abu da ake yiwa Hakimai da Dagatai, bai sanya sunyi kasa a guiwa wajen kawo rahoton abubuwan dake faruwa ba ga jami'an tsaro."

Sarkin ya bukaci gwamnatin tarayya ta kara bawa kwamitin ta NEDC kudi, sakamakon matsalolin da suka faru a jihar da suka yi sanadiyyar lalata abubuwa da dama a jihar.

Ya bayar da tabbacin cewa a yadda sojoji suke kaiwa 'yan ta'addar hari a yanzu, wannan rikici ya kusa ya zama tarihi.

Ya ce wannan tawagar ta zo jihar ne domin gani da ido akan irin ayyukan da kwamitin ta NEDC take yi na tsawon shekara daya a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel