Ku bamu milyan 20 mu saki yaranku: Masu Garkuwa da dalibai a Kaduna sun bukaci kudin fansa

Ku bamu milyan 20 mu saki yaranku: Masu Garkuwa da dalibai a Kaduna sun bukaci kudin fansa

Masu garkuwa da mutanen da sukayi awon gaba da daliban makarantar Prince Academy dake unguwar Dabam-Kasaya a karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna sun bukaci kudin fansa milyan ashirin.

Sun lashi takobin cewa sai an biya kudin ne zasu sake dalibai hudu da malama daya.

Legit Hausa ta ruwaito muku yadda aka sace daliban makaranta dake shirin jarabawa a makon jiya, ranar Talata.

Yan bindigan da suka dira garin misalin karfe 8:30 na safe sun kashe wani matashi mai suna Benjamin Auta.

Wani shugaban matasa, Akila Luka Barde, ya bayyana cewa masu garkuwan sun kira iyalan daliban ranar Asabar inda suka bukaci kudin fansa, Daily Trust ta ruwaito.

"Lallai sun kira iyalan kuma sun bukaci milyan 20 kudin fansansu. Bamu san yadda suke son talakawa su samu kudin masu yawa irin haka ba. Amma muna addu'a." Yace.

Luka ya ce har yanzu suna cigaba da tattaunawa da barayin mutanen.

Ku bamu milyan 20 mu saki yaranku: Masu Garkuwa da dalibai a Kaduna sun bukaci kudin fansa
Ku bamu milyan 20 mu saki yaranku: Masu Garkuwa da dalibai a Kaduna sun bukaci kudin fansa
Source: Facebook

KU KARANTA: Yan bindiga sun kai hari Kaduna, sun kashe mutane 2 tare da awon gaba da dan sanda

A ranar 25 ga Agusta, mun kawo muku cewa wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun shiga gidajen mazauna yankin Damba-Kasaya da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

An gano cewa, 'yan bindigar sun iza keyar yara uku 'yan makaranta da ke bita a kan jarabawar kammala aji uku na sakandare da za su fara.

Bawa Wakili, wani mazaunin yankin ya zanta da jaridar The Cable inda yace 'yan bindigar sun zo "da yawansu kamar yadda suka saba", kuma sun dinga harbi har suka kammala abinda suka yi niyya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel