Ciwon zuciya ya kama amarya a daidai lokacin da ake tsaka da bikinta

Ciwon zuciya ya kama amarya a daidai lokacin da ake tsaka da bikinta

- Amarya daga Sadot Negav a yankin kudancin Isra'ila ta fadi a daidai lokacin bikinta

- Wasu daga cikin 'yan bikin ma'aikatan lafiya ne, sune suka ceto rayuwarta

- Amaryar dai na cikin wani mawuyacin hali a cibiyar lafiya ta Soroka dake Beersheba

Wata mata mai shekaru 33 na kwance a asibiti rai a hannun Allah, bayan ta kamu da ciwon zuciya a daidai lokacin da ake tsaka da bikinta a kasar Isra'ila.

Amaryar, da ta fito daga yankin Sadot Negeve a Kudancin kasar ta Isra'ila, ta fadi a gaban 'yan uwa da abokanan arziki da suka halarci bikinta don taya ta murna a ranar Lahadi 30 ga watan Agusta.

Ciwon zuciya ya kama amarya a daidai lokacin da ake tsaka da bakinta
Ciwon zuciya ya kama amarya a daidai lokacin da ake tsaka da bakinta
Source: Depositphotos

A rahoton da IsraelHayom ta fitar, wasu daga cikin 'yan bikin dake aiki a bangaren lafiya sune suka yi kokarin ceto rayuwar amaryar har lokacin da motar asibiti ta karaso wajen.

Amaryar wacce ita ma likita ce, an garzaya da ita zuwa babbar cibiyar lafiya ta Soroka dake Beersheba, cikin mawuyacin hali.

KU KARANTA: Barayi sun sace mai jego kwana hudu bayan ta haihu a jihar Taraba

Anyi ta kokarin ceto rayuwar amaryar kafin su karasa asibitin, cewar wata majiya a kasar. A yanzu haka dai tana asibitin ana lura da ita.

An gabatar da bikin auren ne a wani dan karamin lambu sakamakon rufe wuraren gabatar da biki da gwamnatin kasar ta saka aka yi saboda annobar coronavirus.

Ya zuwa yanzu dai akwai kimanin mutum 113,000 da suka kamu da cutar ta coronavirus, da kuma mutum 906 da suka mutu duka sakamakon cutar a kasar ta Isra'ila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel