Tashin hankali: Yadda aka zaro wani maciji mai tsawon gaske daga cikin wata mata, bayan ya shiga ta bakinta lokacin da take bacci

Tashin hankali: Yadda aka zaro wani maciji mai tsawon gaske daga cikin wata mata, bayan ya shiga ta bakinta lokacin da take bacci

- Matar ta fara jin rashin lafiya bayan macijin ya shiga cikinta a kauyen Levashi

- Likitoci sun cire macijin bayan sun sanya wani abu a bakinta a asibiti

- An sanya macijin a cikin wani botiki, amma ba a tabbatar da ko yana da rai ko babu ba

Wannan abun tashin hankali da yawa yake, likitoci sun zaro wani maciji mai tsawon kamu 4 daga bakin wata mata a kasar Rasha.

A rahoton da Daily Mail ta fitar, macijin ya shiga cikinta ne a lokacin da take tsakiyar bacci a tsakar gidanta dake kauyen Levashi a Dagestan.

A lokacin da ta fara jin rashin lafiya sai ta garzaya zuwa asibiti, inda aka fara duba lafiyarta.

Tashin hankali: Yadda aka zaro wani maciji mai tsawon gaske daga cikin wata mata, bayan ya shiga ta bakinta lokacin da take bacci
Tashin hankali: Yadda aka zaro wani maciji mai tsawon gaske daga cikin wata mata, bayan ya shiga ta bakinta lokacin da take bacci
Source: Facebook

A lokacin da ake cire macijin, an nuno likitan lokacin da yake aikin cire macijin, inda ya sanya wani abu mai tsawo a bakinta ya zaro macijin.

A yayin da ake gabatar da wannan aiki kan matar, daya daga cikin likitocin an jiyo shi yana cewa: "Bari mu ga wane irin abu ne a nan."

Bayan ciro macijin wata mace daga cikin likitocin ta dauki macijin da hannunta cikin yanayi na tsoro da mamaki.

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Kungiyar Malaman jihar Kano da kungiyoyin Sakai, sun goyi bayan hukuncin kisan da kotu ta yanke

Daga baya an sanya macijin a cikin wani botiki, amma dai ba a gano ko macijin yana da rai ko babu ba.

Ba a bayyana kowacece matar da lamarin ya faru da ita ba, sannan kuma ba a bayyana halin da take ciki ba.

Mutane a kauyen na Levashi, sunce irin wannan lamari yana faruwa a lokuta da dama, kuma sun shawarci mutane da yawa akan su daina kwanciya a waje, saboda a kowanne lokaci macijin zai iya shiga bakin mutum.

Kauyen na Levashi yana da yawan mutane 11,500, wasu mutane sunce wannan abu da ya shiga cikin matar zai iya zama ba maciji bane, sai dai kuma dukkan alamu sun nuna cewa maciji ne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel