Ministan aikin gona ya ce an kammala gina kamfanin takin Aliko Dangote

Ministan aikin gona ya ce an kammala gina kamfanin takin Aliko Dangote

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce an kawo karshen aikin kamfanin takin zamanin da mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya ke ginawa a jihar Legas.

Ministan harkar gona da cigaban karkara, Alhaji Muhammad Sabo Nanono, ya kai ziyara domin zagayawa ya ga wannan kamfani na Alhaji Aliko Dangote.

Jaridar Vanguard ta ce ministan ya kai wannan ziyara ne a karshen makon jiya, inda ya yabawa ‘dan kasuwar, ya ce kamfaninsa zai taimakawa harkar noma.

Mai girma ministan ya yabawa Aliko Dangote da ya sa kudinsa wajen harkar takin zamani, wanda hakan zai sa farashin buhun taki ya rage kudi a Najeriya.

“Gwamnatin tarayya ta na son ganin ‘yan Najeriya su na da abin da za su ci. Za mu iya cin ma wannan buri ne kawai idan mu na da isasshen taki a kasa.”

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta dawo da tallafin mai a Najeriya

Ministan aikin gona ya ce an kammala gina kamfanin takin Aliko Dangote
Ministan aikin gona Alhaji Muhammad Sabo Nanono
Source: Twitter

Muhammad Sabo Nanono ya kara da cewa: “Ina matukar alfahari da abin da Aliko Dangote ya ke yi a kasar nan. Babu wanda ya ke yin irin rabin abin da ya ke yi.”

“Karfin takin Dangote ya isa ya canza yadda ake amfani da taki a kasar nan. Za mu dafa masa, mu kuma bada gudumuwa ga kokarin da ya ke yi.” Inji Nanono.

“Babu shakka takin Dangote zai taimakawa mutane da gwamnati.” Mai girma ministan ya ce kananan ‘yan kasuwa za su amfana da takin na Dangote.

Wani darekta na kamfanin Dangote, Devakumar Edwin, ya ce su na da dakin bincike inda ake auna karfin takin zamanin tare da duba kyawun kasar noma.

Devakumar Edwin, yace da kamfanin zamanin na Dangote, Najeriya za ta samu isasshen taki, har a rika fita da buhuna zuwa sauran kasashen Nahiyar Afrika.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel