'Yan sa kai sun fatattaki masu garkuwa da mutane, sun kashe 3 a take

'Yan sa kai sun fatattaki masu garkuwa da mutane, sun kashe 3 a take

- Rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da karbar gawawwakin wasu mutum 3 da 'yan sa kai suka kashe a Yobe

- Ana zargin mutum ukun da zama masu garkuwa da mutane bayan sace wani mutum daya da suka yi suka shiga daji

- 'Yan sa kan sun yi nasarar bin 'yan bindigar har cikin daji inda suka kashe uku, sannan suka damko uku tare da mika wa 'yan sanda

Jami'an 'yan sandan jihar Yobe sun tabbatar da cewa, sun karba gawawwakin wasu mutum 3 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne wadanda 'yan sa kai suka fatattaka suka kashe.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya sanar da gidan talabijin na Channels cewa, an kashe wadanda ake zargin da safiyar Lahadi.

Ya sanar da hakan ne yayin bada bayani a kan harin. Duk da dai, a lokacin rubuta wannan rahoton babu gamsasshen bayani, rundunar 'yan sandan ta ce tana kokarin samun cikakken bayanin.

Abdulkarim ya ce, "A safiyar yau Lahadi ne muka samu rahoton harin da aka kai wa wani kauye mai suna Murfa Kalam inda 'yan sa kai suka kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

'Yan sa kai sun fatattaki masu garkuwa da mutane, sun kashe 3 a take
'Yan sa kai sun fatattaki masu garkuwa da mutane, sun kashe 3 a take. Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

KU KARANTA: Jerin jiga-jigan APC da ke zawarcin shugabancin jam'iyyar da manyan mukamai

"A halin yanzu, an ajiye gawawwakinsu a asibitin kwararru da ke Damaturu yayin da ake ci gaba da bincike."

Kamar yadda mazauna yankin suka sanar, wata kungiyar 'yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun shiga yankin Dungurum da ke kauyen Murfa Kalam.

A yayin harin a karamar hukumar Damaturu ta jihar, wadanda ake zargin an gano har sun kama mutum daya da zummar garkuwa da shi.

Bayan samun bayanin ne kungiyar 'yan sa kan suka bi hanya tare da fatattakar maharan. A take suka kashe uku sannan wasu suka tsere.

Wata majiya ta sanar da gidan talabijin na Channels cewa, an kama mutum uku da ake zargi kuma tuni an mika su hannun rundunar sojin Najeriya.

Amma kuma, hukumomin rundunar sojin har yanzu basu ce komai a kan lamarin ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel