An kashe mutum 2, da yawa sun jikkata yayin wani rikici da ya barke tsakanin 'yan Shi'a da 'yan sanda a Kaduna
- Wani rikici da ya barke tsakanin 'yan shi'a da 'yan sanda a jihar Kaduna yayi sanadiyyar mutuwar mutum biyu, yayinda da yawa kuma suka ji muggan raunika
- Rikicin dai ya samo asali ne a daidai lokacin da 'yan shi'ar suke gabatar da zanga-zanga akan gwamnati ta sakar musu shugabansu da matarsa da suke tsare tun watan Disambar shekarar 2015.
Mutum biyu daga cikin mabiyan Sheikh Ibrahim Zakzaky, sun rasa ransu sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin jami'an 'yan sanda da su a Kaduna a jiya Lahadi.
Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa an jiyo harbin bindiga akan babbar hanyar Ahmadu Bello Waya a jiya da rana, a lokacin da 'yan sandan suke kokarin tarwatsa dandazon 'yan shi'ar.
'Yan Shi'ar dai sun fito zanga-zanga ne domin kara nuna bukatarsu ta a sakar musu shugaban su Sheikh Ibrahim Zakzaky, da matarsa, Zeenat, wadanda ake tsare dasu tun a watan Disambar shekarar 2015, sakamakon rikicin da suka yi da jami'an hukumar soji a Zaria.
Sai dai kuma, tuni gwamnatin jihar Kaduna ta riga ta haramta wannan kungiya ta kuma hana duk wata zanga-zanga da kungiyar za ta yi a jihar.
Haka kuma, wani babba daga cikin 'yan kungiyar ya sanarwa da Daily Trust cewa biyu daga cikin 'yan kungiyar su sun mutu sakamakon wannan rikici da suka yi a jiya, inda da yawa kuma suka ji muggan raunika.
KU KARANTA: An bindige jigon jam'iyyar PDP a yayin da yake dawowa daga wajen taron jam'iyya
"Maganar nan da muke daku, a yanzu muna kara matsin lamba akan sakin shugaban mu. Akwai biyu daga cikin mambobin mu da 'yan sanda suka kashe. Wasu da yawa kuma daga cikinmu sunji muggan raunika," ya ce.
Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, ya ce har ya zuwa lokacin bai samu wani rahoto akan wannan lamari ba.
A cewarsa: "Na kira DPO dake kula da yankin, bai daga wayata ba; akwai yiwuwar yana kokarin kwantar da tarzomar da ta barke ne a lokacin. Amma da zarar na samu labari yadda lamarin yake zan kira ku."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng