Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna)

Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna)

Sarkin Abaji kuma shugaban majalisar sarakunan babban birinin tarayya, Mai martaba, Alhaji Adamu Baba Yunusa, ya karba bakuncin Mai Martaba Sarkin kano, Dr. Aminu Ado Bayero, a fadarsa da ke Abuja a ranar Asabar.

Dr. Bayero, wanda ya isa fadar Sarkin Abajin tare da tawagarsa wurin karfe 7 na yamma, an shigar da shi har cikin fadar basaraken inda yake karbar sarakunan gargajiya.

Sarkin , Alhaji Adamu Baba Yunusa, ya nuna murnarsa da farin cikin ziyarar da Sarkin Kano ya kai wa masarautarsa, jaridar Daily Trust ta wallafa.

Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna)
Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna). Hoto daga Masarautar Kano
Source: Twitter

Ya ce babu shakka wannan ziyara ce mai cike da tarihi. Ya ce hakan ya nuna yadda masarautar Kano ta dauka masarautarsa da muhimmanci.

Ya ce masarautun Abaji da Kano tun asali suna da alaka mai karfi. Kuma a can wani lokaci da ya shude, Dr Abudllahi Umar Ganduje na jihar Kano ya taba aiki da majalisar masarautar.

Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna)
Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna). Hoto daga masarautar Kano
Source: Twitter

KU KARANTA: Halin da lafiyar Aisha Buhari da Mamman Daura ke ciki

Basaraken ya yi amfani da wannan damar wurin kira ga sarkin Kano a kan bada goyon baya da tallafi wurin karasa ginin babban masallacin Abaji wanda ake ginawa fiye da shekaru 20 da suka shude.

Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna)
Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna). Hoto daga masarautar Kano
Source: Twitter

A yayin martani, Sarkin Kano ya mika godiyarsa ga Sarkin Abaji da 'yan majalisar sarakunan tare da masu ruwa da tsaki na masarautar da suka karrama shi.

Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna)
Sarki Aminu Ado-Bayero ya sake kai wa wani babban basarake ziyara (Hotuna). Hoto daga masarautar Kano
Source: Twitter

Ya ce tuni dama masarautar Abaji gida ce gareshi. Ya kara da bada tabbacin cewa zai yi iyakar kokarinsa wurin tabbatar da an shawo kan manyan matsalolin da ke addabar masarautar, ciki har da karasa ginin babban masallacin yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel