Halin da lafiyar Aisha Buhari da Mamman Daura ke ciki

Halin da lafiyar Aisha Buhari da Mamman Daura ke ciki

Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari, da dan uwansa, Mamman Daura sun kasance a kanun labarai a cikin kwanakin nan.

Labarin mai dadi a nan shine, Aisha Buhari ta dawo kasar nan cike da koshin lafiya daga birnin Dubai inda ta je jinya.

Hakazalika, a bangaren Daura, an gan shi a wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani yana cikin koshin lafiya.

Aisha Buhari ta yi amfani da wannan damar yayin da ta dawo, inda ta mika godiyarta game da addu'o'in da 'yan Najeriya suke mata yayin da ta tafi jinya.

Aisha Buhari ta bayyana hakan ne a shafinta na Tuwita da daren Asabar, 22 ga Agusta, 2020. Yayinda dawowarta daga Dubai, Aisha ta bayyana cewa jirginsu ya dan samu mishkila cikin hazo amma matukan sun samu daman shawo kan lamarin.

Ta ce, "Ina cikin koshin lafiya kuma tuni na dawo gida. Ina amfani da wannan damar wurin mika godiyata ga 'yan Najeriya da suka dinga mana addu'o'i tare da fatan alheri a yayin da naje jinya."

"Yayinda muke hanyar dawowa, jirgin mayakan saman Najeriya ya samu matsala cikin hazo amma babban matukin jirgin da abokan aikinsa sun samu nasarar shawo kan lamarin.

"Ina jinjina da godiya kan matukan jirgin bisa namijin kokarin da sukayi."

Halin da lafiyar Aisha Buhari da Mamman Daura ke ciki
Halin da lafiyar Aisha Buhari da Mamman Daura ke ciki. Hoto daga Channels TV
Source: UGC

KU KARANTA: Lauyan da yayi murnar mutuwar Kyari da Funtua, da fatan mutuwar Buhari ya rasu

A ranar 7 ga Agusta, mun kawo muku rahoton cewa an garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, kasar UAE don jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas, Daily Trust ta ruwaito.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Yayinda ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata daya bayan ta'aziyyar.

Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidar kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel