Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa

Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa

Duk da ba kamar yadda aka san Boko Haram ba, wacce ta dade tana cin karenta babu babbaka a yankin arewa maso gabas na kasar nan, amma babu shakka Darul-Salam kungiyar 'yan ta'adda ce mai cike da hatsari.

An fatattaketa daga jihar Neja kusan shekaru 11 da suka gabata, yayin mulkin tsohon gwamna Mua'azu Babangida Aliyu.

Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa
Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Kungiyar ta sake kafuwa a yankin Uttu da ke karamar hukumar Toto da jihar Nasarawa a yankin arewa ta tsakiya ta Najeriya, a kalla nisan kilomita 14 daga babban birnin kasar Najeriya.

Amma kuma, bayan aikin zakukaran dakarun sojin kasar nan na ranar Laraba, 26 ga watan Augustan 2020 karkashin rundunar Operation Whilr Stroke, sun ceto sama da mutum 410 da suka hada da kananan yara da mata daga kungiyar.

Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa
Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Wani shugaba a yankin wanda ya bukaci a boye sunansa yayin bayani ga Daily Trust, ya ce kungiyar Darul-Salam ta fara mamaye dajin da ke da kusan fadin mita 600 da tsayi.

Sun fara bayyana kansu a matsayin makiyaya wadanda suka zo noma da kiwo tare da kafa addinin Islama.

Kamar yadda yace, manoman yankin sun fara korafi a kan kungiyar bayan da suka gano cewa shanunsu na cinye musu amfanin gonakinsu.

"Sun fara zuwa babu yawa tare da shanu inda suke kafa sansaninsu har zuwa lokacin da aka fara korafi a kan barnar da shanunsu ke yi a gonakin jama'a,"yace.

"Bayan wani lokaci, kungiyar ta cigaba da samun mambobi, lamarin da yasa Fulanin da ke kusa da sansaninsu suka bar yankin. Hakan ya saka wasi-wasi a zukatan jama'a a kan abinda ya kawo su dajin," yace.

Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa
Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Lauyan da yayi murnar mutuwar Kyari da Funtua, da fatan mutuwar Buhari ya rasu

Wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce sun fara zargin jama'ar ne bayan da jama'ar suka yi garkuwa da wasu masu yin itace da kuma manoma.

Ya ce kungiyar ta gallabi jama'a tun bayan da suka kara yawa. Wasu daga cikinsu sun fara saka kayan sojojin kuma suna sace mutane a gidaje, gonaki da kuma manyan hanyoyin da suka hada da babban titin Abuja zuwa Lokoja.

Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa
Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Ya kara da cewa, lamarinsu ya zama abun tsoro tun bayan da suka fara shiga kauyukan yankin da bindigogi kirar AK 47 a kan babura domin siyan kayan abinci.

An gano cewa, kungiyar ta fara bai wa kananan yara horarwa a wurin harbi, hada bama-bamai da kuma yadda za su dasa su a cikin sansanin.

An gano cewa, wani sashin na sansanin ya kasance makaranta inda ake koyar da kananan yaran da wasu wadanda suka kamo karatun Islamiya.

Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa
Hotuna: Yadda kungiyar Darul-Salam ta kafu a jihar Nasarawa. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Wata matar aure mai mai tsohon ciki, wacce dakarun sojin suka ceto mai suna Khadija Abdullahi, ta bayyana yadda 'yan ta'addan suka kashe mata miji a Gombe.

Sun daukota zuwa Nasarawa inda daya daga cikinsu ya dirka mata ciki. Tana da 'ya'ya mata biyu kuma tare aka daukosu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel