Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya warke daga cutar korona

Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya warke daga cutar korona

- Kayode Alabi, mataimakin gwamnan jihar Kwara ya warke daga cutar coronavirus

- Alabi tare da matarsa sun kamu da cutar korona makonni uku da suka gabata

- Kakakin kwamitin COVID-19 a jihar Kwara kuma babban sakataren labaran Gwamna AbdulRaman Abdulrazaq, Rafiu Ajakaye ne ya bayyana haka

Mataimakin gwamnan jihar Kwara, Kayode Alabi ya warke daga cutar coronavirus makonni uku bayan kamuwa da muguwar annobar.

Alabi ya harbu da cutar korona kwanaki biyu bayan ya cika shekaru 57 a ranar 1 ga watan Agusta, tare da matarsa, Abieyuwa, PMNews ta ruwaito.

Sai dai, kakakin kwamitin COVID-19 a jihar Kwara kuma babban sakataren labaran Gwamna AbdulRaman Abdulrazaq, Rafiu Ajakaye, a wani jawabi a ranar Asabar, ya bayyana cewa mataimakin gwamnan ya warke.

KU KARANTA KUMA: Ina caccakar sojoji ne domin na taimake su wajen kara zage damtse, in ji Zulum

Ya ce: “A yammacin ranar Juma’a, 28 ga watan Agusta, sakamakon gwajin da aka sake yi wa mai girma mataimakin gwamnan jihar Kwara kuma Shugaban kwamitin korona na jihar, Mista Kayode Alabi ya nuna baya da cutar.

Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya warke daga cutar korona
Mataimakin gwamnan jihar Kwara ya warke daga cutar korona Hoto: PMNews
Source: UGC

“Hakan na nufin mataimakin gwamnan ya warke daga cutar kuma zai dawo bakin aikinsa.

“Gwamnatin na godiya ga jama’a a kan gudunwarsu da addu’o’i, da kuma tawagar likitoci kan kokarinsu.

"Gwamnatin na kuma yi wa dukkanin marasa lafiyan da suka rage fatan samun waraka, ciki harda matar mataimakin gwamnan, yayinda take kira ga jama’a da kada su yi matsi da matakin kare kai domin dakile cutar.”

A gefe guda, Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 160 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:27 na daren ranar Jumaa 28 ga Agustan shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 160 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Plateau-44

Lagos-27

Katsina-18

Edo-15

FCT-14

Ondo-10

Oyo-9

Kwara-6

Abia-4

Nasarawa-4

Kano-3

Ekiti-2

Kaduna-2

Kebbi-1

Ogun-1

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel