FG ta ce ba za ta kara lamuntan cin zarafin ‘yan Najeriya a Ghana ba
- Gwamnatin tarayya ta gargadi hukumomin kasar Ghana cewa ba za ta kara lamuntan cin zarafin ‘yan Najeriya a wannan kasar ba
- Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed ne ya yi gargadin
- Mohammed ya ce gwamnatin tarayya na ta tara bayanai kan rashin kyautatawa da hukumomin Ghana ke nunawa ‘yan Najeriya
- Daga cikin rahin kyautatawar da ake zargin kasar ta Ghana da yi wa Najeriya harda rushe ginin ofishin jakadancinta na kasar
Gwamnatin tarayya ta gargadi hukumomin kasar Ghana cewa ba za ta kara lamuntan cin zarafin ‘yan Najeriya a wannan kasar ba.
Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed a cikin wani jawabi a ranar Juma’a, 28 ga watan Agusta, ya ce gwamnatin tarayya na tara bayanai kan rashin kyautatawar da hukumomin Ghana ke nunawa ‘yan Najeriya, jaridar The Cable ta ruwaito.
Ministan ya ce wasu daga cikin rashin kyautatawar da hukumomin kasar Ghana ke nunawa ‘yan Najeriya sun hada da kwace ginin hukumar Najeriya a No. 10, Barnes Road, Accra.
KU KARANTA KUMA: Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa
Ya kuma bayyana zargin rushe ginin hukumar Najeriya a No. 19/21 unguwar Julius Nyerere, East Ridge, Accra da kuma yawan koro ‘yan Najeriya gida daga Ghana.

Asali: UGC
Mohammed ya ce Najeriya ta nuna bacin rai kan yadda ake cin zarafin al’umman kasarta sannan ake masu ba’a, inda ya ce ba za a sake lamuntan cin mutuncin ‘yan Najeriya ba ta kowani irin fasali
A halin da ake ciki, ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa farmakin da ake kai wa masu kasuwanci ba bisa ka'ida ba a Ghana ana yi ne saboda kokarin cimma manufar siyasa.
KU KARANTA KUMA: Ina caccakar sojoji ne domin na taimake su wajen kara zage damtse, in ji Zulum
A cikin jerin sakonnin da ta wallafa a shafin Twitter, ministar ta bayyana kalaman a matsayin "abin takaici" sannan ta bayyana cewa gwamnatin Ghana ba ta da nufin cuzguna wa 'yan wata kasa.
Dokokin Ghana dai sun haramta wa 'yan kasashen waje bude shagunan sayar da daidaikun kayayyaki, musamman ma a yankunan da ake kasuwanci.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng