Shin da gaske El-Rufa'i ya kai Fasto kotu don yace ba zai taba mulkan Najeriya ba?

Shin da gaske El-Rufa'i ya kai Fasto kotu don yace ba zai taba mulkan Najeriya ba?

IKIRARI:

A ranar 23 da 24 ga Agusta, wasu jaridun Najeriya (Musamman The Source, The Daily Times da Sahara Reporters) sun ruwaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da Fasto Abiodun Ogunyemi, a kotu don yace El-Rufa'i ba zai taba zaba shugaban kasan Najeriya ba.

GASKIYAN LAMARI:

Wannan karya ne. Takardun hujjoji sun nuna cewa babu gaskiya cikin labaran cewa ana gurfanar da faston ne kan maganar da yayi cewa El-Rufa'i ba zai taba zaman shugaban kasa ba.

BINCIKEN GASKIYA:

pREMIUM TIMES ta katabta cewa lallai da gaske ne Bishap Ogunyemi yayi magana ranar 23 ga Nuwamba, 2019 cewa gwamna El-Rufa'i ba zai taba shugaban kasan Najeriya ba.

Hakazalika gaskiya ne an gurfanar da shi a gaban kotun Majistare dake Kaduna ranar 4 ga Agusta. Ya sake komawa ranar 17 inda Alkalin ya dage zaman zuwa 28 ga Oktoba.

Amma takardun da DUBAWA da PREMIUM TIMES suka bibiya sun nuna cewa ana gurfanar da Faston ne bisa kazafi, barazana da karya, ba don ya zagi gwamna El-Rufa'i ba.

Hukumar yan sanda ta zargi Faston da kazafin da yayi a hirarsa da jaridar Punch da aka wallafa ranar 15 ga Disamba 2015 inda ya yiwa gwamna kazafin cewa:

- El-Rufa'i gayyacesa ofishin gwamna don dana masa tarko da sunan tattaunawa da shi kan lamarin rusa cocin Zaria

- Ranar da gwamna ya gayyaci shugaban Adara ne aka kasheshi yayinda yake hanyar zuwa wajen gwamnan

- Wai gwamnan na fushi da shi da kungiyar Kiristocin Najeriya CAN kan kalaman da sukayi kan shirin rusa cocin Zariya

- Wai lokacin da gwamna ya kasa cimman manufarsa, sai aka gayyacesu Kano saboda a tareshi a hanya kuma a tilastashi baiwa gwamna hakuri, kuma shi ba zai taba hakan ba

Bayan wannan, Faston na fuskantar karar da dan uwansa, Bishop Ali Buba, ya shigar kansa.

Ya yiwa Bishop Ali Buba kazafin cewa dan leken asirin Musulmai ne saboda Bafulatani ne.

KARANTA WANNAN: Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa

A KARSHE

Rahotannin da wadannan jaridu suka yada cewa El-Rufa'i ya shiga da Faston kotu karya ne kuma yaudara ne.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel