Ganduje ya nada sabbin alƙalai 6 a Kano (Sunaye)

Ganduje ya nada sabbin alƙalai 6 a Kano (Sunaye)

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya rantsar da sabbin alkalai shida a babban kotun jihar Kano domin rage jinkirin da ake samu wurin yanke shari'a.

Attoney Janar na jihar, Mista Muhammad Lawal, ne ya bawa sabbin alkalan rantsuwar kama aiki a ranar Juma'a a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito

Sabbin alkalan da aka rantsar sune: Abubakar Maiwada, Maryam Sabo, Zuwaira Yusuf A, Jamilu Sulaiman, Sunusi Ma’aji da Hafsat Yayha Sani.‎

Ganduje ya nada sabbin alkalai 6 a Kano (Hotuna)
Ganduje ya nada sabbin alkalai 6 a Kano (Hotuna)
Source: Twitter

Ganduje ya ce an rantsar da sabbin alkalan ne saboda kwazonsu da jajircewa bayan sun yi nasarar cin gwajin da aka musu kuma kwamitin koli na alkalai na kasa, NJC, ta amince a nada su.

Gwamnan ya ce nadin da aka yi musu zai kara adadin alkalai a jihar kuma hakan zai rage tsawon lokacin da ake dauka kafin yin sharia tare da bawa alkalan daman samun natsuwa suyi adalci.

DUBA WANNAN: Mutum 16 sun mutu yayin da babbar mota ta murƙushe ƙananan motocci 3 a Zamfara

Ya ce bangarorin gwamnati uku za su hada kai suyi aiki tare domin amfanin al'ummar jihar.

Ganduje ya bukaci sabbin alkalan su kasance masu riko da gaskiya da amana su kuma kare mutunci da kimar aikin alkalanci.

Gwamna Ganduje ya kuma rantsar da Alhaji Aminu Bahaushe a matsayin sakataren dindinin aka kuma tura shi zuwa ma'aikatar gidaje da sufuri kamar yadda kamfanin dillancin labaran NAN ya ruwaito.

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Bashir Tijjani Babajo a matsayin direktan sashin ayyuka na hukumar inshoran manoma ta Najeriya, NAIC, karo na farko na shekaru huɗu.

Leadership ta ruwaito cewa shugaban kasar ya kuma sabunta naɗin Philip Ashinze a matsayin babban direktan sashin kuɗi da mulki na hukumar karo na biyu.

Legit.ng ta gano cewa naɗe-naɗen za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2020.

Sanarwar da direktan watsa labarai na ma'aikatar noma da cigaban karkara, Theodore Ogasziechi ya raba wa manema labarai ta ce shugaban kasar ya sanar da amincewarsa na cikin wasikar da ya aike wa ministan Noma, Muhammad Sabo Nanono mai lamba SH/COS/42/3/A/988 mai ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikatar fadan shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Da ya ke taya wadanda aka yi wa nadin murna, ministan ya yi kira garesu su yi amfani da kwarewarsu ta aiki domin cigaba da aiwatar da tsare tsaren NAIC bisa doka da oda.

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ce ta mallaki NAIC, kuma an kafa ta ne domin bawa manoman Najeriya inshora.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel